Gwamna Ya Tona Asirin Yan Bindiga, Ya Bayyana Inda Suka Fito da Manufar Zuwan Su Najeriya

Gwamna Ya Tona Asirin Yan Bindiga, Ya Bayyana Inda Suka Fito da Manufar Zuwan Su Najeriya

  • Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja, yace mafi yawan yan bindiga da suka hana arewa zaman lafiya ba yan Najeriya bane
  • Gwamnan yace an ɗakko hayar su ne domin su canza rayuwar yan ƙasa zuwa tashin hankali
  • Hakanan gwamnan ya gana da iyayen ɗalibai 136 da aka sace a makarantar islamiyyar Salihu Tanko, Tegina

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa mafi yawancin yan bindigan da suka addabi yankin arewa daga ƙasashen waje suka fito, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

Gwamnan yace ya zama wajibi a kan yan Najeriya su yi iyakar bakin ƙoƙarin su wajen ganin yan bindiga ba su yi nasara akan su ba.

Gwamna Bello ya faɗi haka ne yayin ƙaddamar da haɗakar wakilan jami'an tsaro 1000 na musamman domin tabbatar da an ƙuɓutar da ɗaliban islamiyyar Salihu Tanko, Tegina, ƙaramar hukumar Rafi.

Gwamnan Neja a fadar Sarkin Kagara
Gwamna Ya Tona Asirin Yan Bindiga, Ya Bayyana Inda Suka Fito da Manufar Zuwan Su Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yace: "Mafi yawancin waɗannan yan bindigan daga wajen Najeriya suke, an ɗakko su ne su hana mu zaman lafiya. Wannan ba ya cikin al'adar fulani su aikata irin waɗannan munanan ayyukan."

Legit.ng hausa ta gano cewa jami'an tsaron da gwamnan ya ƙaddamar sun ƙunshi wakilai daga yan sanda, sojoji, yan sa kai da jami'an NSCDC.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Ƙasa Kan Yan Boko Haram a Dajin Borno

Gwamna Bello Ya gana da iyayen ɗaliban da aka sace

Mr. Bello ya gana da iyayen ɗalibai 136 da yan bindiga suka sace a makarantar Salihu Tanko dake Tegina a fadar Sarkin Kagara, Alhaji Bello Gunna.

Gwamnan ya jajanta musu kan lamarin, sannan ya roƙi su cigaba da hakuri, domin gwamnatinsa zata yi duk abinda ya kamata wajen ganin ɗaliban sun dawo cikin ƙoshin lafiya.

Yace: "Duk da mun cire maganar biyan kuɗin fansa, amma lokaci yayi da gwamnati zata ɗauki duk matakin da ya kamata domin magance harin yan bindiga."

"Ɓarayin ba su da mutunci, Amma gwamnati zata ɗau mataki a kan su.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram Yayin da Suka Kai Hari Sun Hallaka da Dama a Borno

Sojoji sun samu nasarar daƙile harin yan ta'addan Boko Haram a Ƙunmshe, jihar Borno, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Kakakin sojin yace an yi gumurzu sosai tsakanin sojojin da yan ta'addan waɗanda suka zo da motocin yaƙi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel