Matsalar Tsaro Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina

Matsalar Tsaro Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina

  • Yan bindiga sun kashe matar tsohon kwamishinan ƙananan hukumomin jihar Oyo, Mrs. Olayemi Odetomi
  • Mijin matar, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ogbomoso ne, kuma tsohon kwamishina a jihar Oyo
  • Kakakin yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da lamarin, yace a halin yanzun ana bincike

Wasu yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun kashe, Mrs. Olayemi Odetomi, matar tsohon kwamishinan ƙananan hukumomin jihar Oyo, Peter Odetomi, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: PDP Ta Rushe Majalisar Shugabanninta Awanni Kaɗan Kafin Zaɓe

Rahotanni sun bayyana cewa matar mai kimanin shekara 66 a duniya an kashe ta ne a gidanta dake yankin Bodija-Ashi, Ibadan, jihar Oyo da safiyar ranar Jumu'a.

Yan bindiga sun kashe matar tsohon kwamishina
Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mijin matar, Peter Odetomi, wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ogbomoso ne, ya riƙe muƙamin kwamishina a zamanin mulkin marigayi Abiola Ajimobi.

Sai-dai wasu mutane sun bayyana cewa yan fashi ne suka hallaka, Mrs. Oderomi, wasu kuma na cewa wasu ne suka kashe ta ba gaira ba dalili.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Tawagar Yan Ƙwallon Najeriya da Kyautar Sabbin Gidaje

Yan Sanda sun tabbatar da kisan Mrs.Odetomi

Kakakin hukumar yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace jami'an yan sanda sun fara gudanar da bincike.

Yace: "Marigayya Olayemi Odetomi, ta rasa ransa nan take yayin harin da wasu yan fashi suka kai gidanta da sanyin safiyar ranar Jumu'a 25 ga watan Yuni."

"Zamu cigaba da bayar da bayanin binciken da muka gudanar da zarar an samu wani cigaba."

A wani labarin kuma Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, ya bayyana cewa shugabannin fulani ba su da hannu a sace ɗaliban FGC Yauri, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Gwamnan yace waɗanda suka sace ɗaliban fulani ne da suka fi zama a daji yan wata tawaga mai suna renegade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel