Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu

Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu

  • Jami'an yan sanda sun samu nasarar cafke wata tawagar masu garkuwa da mutane a jihar Ekiti
  • Ɓarayin sun sace wani ɗalibi dake karatu a kwalejin fasaha ta Crown dake Ado Ekiti, inda suka karɓi kuɗin fansa miliyan N2m
  • Daga cikin waɗanda aka kama ɗin akwai abokan karatun wanda aka sace mutum 10

Rundunar yan sanda ta cafke ɗaliban kwalejin fasaha ta Crown dake Ado Ekiti da zargin garkuwa da abokin karatunsu, Akiode Akinyemi, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Waɗanda aka kama ɗin sun karɓi kuɗin fansa daga iyalan ɗalibin da suka kai kimanin naira miliyan N2m.

KARANTA ANAN: Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram, Sun Kuɓutar da Matafiya da Dama

Kakakin yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da lamarin, yace waɗanda ake zargiin sun sace ɗalibin ne tun 19 ga watan Yuni, amma da farko ba'a kawo wa yan sanda rahoto ba.

Dalibai 10 sun yi garkuwa da abokin karatunsu a Ekiti
Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa tawagar masu garkuwan sun kutsa ɗakin kwanan ɗalibin, inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba'a san shi ba.

Ɓarayin sun karɓi miliyan biyu kuɗin fansa

Bayan tattaunawa a wayar salula tsakanin iyayen wanda aka sace da waɗanda ake zargin, an biya ɓarayin kuɗi naira ₦2,200,000 ta asusun banki kala daban-daban.

Amma jami'an tsaron yan sanda sun samu nasarar bibiyar ɓarayin kuma suka yi ram da mutum 14 a wuri daban-daban.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina

Mr. Abutu, yace: "Daga cikin waɗanda aka kama, mun gano cewa akwai ɗaliban kwalejin fasaha Ado Ekiti, inda ɗalibin da aka sace yake karatu."

"Kwamishinan yan sanda, Tunde Mobayo, ya yi Allah wadai da lamarin, kuma yayi kira ga al'ummar jihar su cigaba da taimakawa jami'an tsaro da bayanai."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Tawagar Yan Ƙwallon Najeriya da Kyautar Sabbin Gidaje

Buhari ya amince a baiwa tawagar yan ƙwallon Najeriya waɗanda suka ci ƙasar AFCON 1994 a Tunusia kyautar gidaje, kamar yadda punch ta ruwaito.

Buhari ya bayyana haka ne a wani jawabi da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel