Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo
- Wasu mutane ɗauke da bindiga sun farmaki ɗaya daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na APC a Ondo
- Hon Dele Isibor, ya rasa ransa ne ranar Litinin sabida raunukan da yaji a harin da yan ta'addan suka kai mishi
- Jam'iyyar APC ta yi Allah wadai da kisan Isibor, ta kuma yi kira ga masu faɗa aji su baiwa gwamnati haɗin kai
Wasu yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun hallaka ɗaya daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a jihar Ondo, Hon Dele Isibor, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Wata Jami'a Ta Kori Ɗalibi Ɗan '500-Level' Saboda Ya Soki Gwamna a Facebook
Isibor ya mutu ne ranar Litinin biyo bayan munanan raunukan da ya samu a yayin harin yan bindigan, kamar yadda punch ta ruwaito.
Marigayi Isibor ya kasance sakataren jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Ose jihar Ondo.
A wani jawabi da kakakin APC, Alex Kalejaiye, ya fitar, yace marigayi Isibor mutum ne mai ƙoƙari da jajircewa wajen kawo cigaba a jam'iyyar APC tun daga tushe.
KARANTA ANAN: Hana Amfani da Twitter: Lai Muhammed Ya Bankaɗo Wani Asirin Twitter a Gaban Yan Majalisa
APC ta yi Allah wadai da kashe Isibor
Kalejaiye, ya bayyana cewa maharan sun farmaki marigayin ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Ifon, hedkwatar ƙaramar hukumar Ose.
Yace: "Jam'iyyar APC ta yi Allah wadai da harin da aka kai masa wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa, kuma a dai-dai lokacin da jam'iyyar mu ke shirye-shirye gangaminta."
"Harin da aka kaiwa Isibor da wani makamancinsa ya ƙara nuna buƙatar kowane mai faɗa a ji a jihar Ondo ya bada gudummuwarsa a ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na kawo ƙarshen matsalar."
A wani labarin kuma Kotun ECOWAS Ta Dakatar da Gwamnatin Buhari Daga Cafke Yan Najeriya Dake Hawa Twitter
Kotun ECOWAS ta dakatar da gwamnatin shugaba Buhari daga hukunta yan Najeriya waɗanda suka hau twitter, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Wannan ya biyo bayan ƙarar da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam SERAP ta shigar gaban kotun tana ƙalubalantar matakin FG.
Asali: Legit.ng