Hotunan yadda jama'ar Zaria suka yi wa 'yan bindiga sallar Al-Qunuti
- Jama'ar garin Zaria sun yi sallolin al-Qunuti kan Allah ya kare su daga 'yan bindiga a garin
- Sun share kwanaki domin sallolin tare da zuba addu'o'i domin neman kariyar Allah garesu
- Mun samo hotunan yadda aka gudanar da addu'o'in wadanda suka gudana a filayen Idi a garin
Al'ummar Zaria sun gudanar da Sallar Al-Qunut da addu'oi tsawon mako daya domin neman saukin rikicin 'yan bindiga masu satar mutane da suka addabi yankin.
Dr Shamsuddeen Aliyu mai yasin garkuwan makarantar Zazzau daya daga cikin wadanda suka jagoranci Sallar da addu'oin ya shaida wa BBC cewa an gudanar da sallolin ne a filayen Idi da ke cikin kwaryar Zaria.
KU KARANTA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa
Ya ce daruruwan mutane ne suka halarci Sallar da zaman addu'oin domin rokon Allah ya yi maganin 'yan bindiga wadanda ya ce sun yi wa garin Zaria kawanya.
A cewarsa:
"Mun ga cewa ba mu da mafita illa mu koma wa Allah mu tuba domin Ya yi mana maganin wadannan 'yan bindigar."
A yau Litinin ne aka rufe addu'oin bayan tsawon kwana shida ana yi a kullum.
Ya ce limamin masallacin juma'a na filin mallamawa ne ya jagoranci Sallar da aka yi a masallacin idi na Tudun wada.
Sarkin Zazzau ya koka kan yadda 'yan bindiga suka mamaye garin Zaria
A kwanakin baya ne sarkin Zaria ya ce 'yan bindiga masu satar mutane sun addabi garinsa musamman bayan harin da suka kai suka saci mutane a garin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Bayanai sun ce maharan dauke da bindigogi ne suka shiga sabuwar unguwar Kofar Gayan inda suka kutsa cikin gidaje suka yi awon gaba da iyalai ciki har da 'yan mata da samari.
Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da 'yan bindiga suka sace dalibai da malamai a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke garin na Zaria.
Kalli hotunan a kasa:
KU KARANTA: Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu
Muna cikin tsaka mai wuya duk da sojojin dake Zaria, Sarkin Zazzau ya koka
A wani labarin, Daily Trust ta ruwaito Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, a ranar Litinin yana cewa garin Zaria na cikin mamayar 'yan ta'adda.
A cewarsa, mazauna garin ba sa iya bacci saboda sace-sacen mutane da ke gudana a tsakanin garin Zariya da kewaye.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, Sarkin ya bayyana lamarin a matsayin abinda ba za a yarda da shi ba don haka ya bukaci gwamnati ta dauki mataki.
Asali: Legit.ng