An Shigar da Korafi wajen INEC domin Neman Hana Tinubu Takarar 2027

An Shigar da Korafi wajen INEC domin Neman Hana Tinubu Takarar 2027

  • Rahotanni sun nuna cewa wata ƙungiya ta nemi hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sake binciken takardun karatun Bola Tinubu
  • A korafin da ta rubuwa hukumar INEC, kungiyar ta yi zargin cewa akwai matsaloli a takardun karatun da Tinubu ya ce ya samu a makaranta
  • Budu da kari, masu ƙorafin sun yi barazanar shigar da hukumar INEC gaban kotu idan ta gaza yin karin haske game da abubuwan da ta gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata ƙungiyar farar hula ta shigar da sabon ƙorafi ga INEC, inda ta nemi a sake buɗe shafin bincike kan takardun da shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da su wajen samun amincewar tsayawa takara a 2023.

Kungiyar CFRPA ce ta shigar da korafin mai ɗauke da kwanan watan 19 ga Yunin 2026 ta hannun haɗakar lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Kalu Agu.

Kara karanta wannan

Kungiya ta taso da batun takardun karatun Tinubu, ta aika wasika ga INEC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da aka ba Bola Tinubu shaidar lashe zaben fitar da gwani na APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ƙungiyar ta nemi INEC ta fayyace sahihancin ko akasin haka na takardar shaidar karatu daga Jami'ar Chicago da shugaba Tinubu ya haɗa da fom ɗinsa.

Korafin da aka yi kan Bola Tinubu

Daga cikin zarge-zargen da ƙungiyar ta yi akwai cewa yayin da Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya yi karatu a Lagos a shekarar 1960 kuma ya kammala a watan Mayun 1970, an kafa makarantar ne a 1974.

Ƙungiyar ta nuna damuwa cewa takardun shaidar firamare da sakandaren da shugaba Tinubu ke nunawa, waɗanda aka ce an yi amfani da su wajen samun gurbin karatu a Chicago, na iya kasancewa na jabu.

Kiran kungiyar ga hukumar INEC

Masu ƙorafin sun roƙi shugaban INEC, kasancewarsa Farfesa a fannin shari'a, da ya yi amfani da ƙwarewarsa da iliminsa wajen warware wannan batu da ya daɗe yana jawo ce-ce-ku-ce game da cancantar takarar Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

APC ta yi magana da 'yan majalisa suka fara maganar Tinubu ya sauka

A cewar ƙungiyar, buƙatar INEC ta yi karin haske ta zama dole duba da tanade-tanaden doka kan gabatar da takardun bogi, musamman sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulkin 1999.

Ta kuma yi magana kan sashe na 285(14), wanda ya tanadi ikon hukumar wajen hana 'yan takarar da ba su cancanta ba shiga zaɓe.

Shugaban INEC, Joash Amupitan
Farfesa Joash Amupitan a ofishin hukumar INEC. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Barazanar maka INEC a kotu

Masu ƙorafin sun yi barazanar ɗaukar matakin shari'a a kan INEC idan ba ta yi karin haske kan cancantar Shugaba Tinubu ba.

Ƙorafin ya ce:

“Mu ƙungiya ce mai zaman kanta da ke fafutukar kare dimokuraɗiyya, haƙƙin ɗan Adam, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma kare muradun jama'a a Najeriya."

The Sun ta rahoto cewa masu korafin sun ce:

“Bisa sashe na 137(1)(g) na kundin tsarin mulkin 1999, duk ɗan takarar da ya gabatar wa INEC takardar bogi bai cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasar Najeriya ba.”

Ana so Tinubu ya sauka a mulki

A wani labarin, mun kawo muku cewa kiran da ake yi wa Bola Tinubu ya yi murabus saboda gaza magance matsalolin tsaro ya shiga zauren majalisa.

Kara karanta wannan

Komai ya fito: An jero abubuwa 18 da Iran da Amurka suka yarda da su

Marasa rinjaye a majalisar wakilai sun yi wani taro da suka bayyana bukatar shugaban kasar ya magance matsalolin Najeriya ko ya sauka.

Sai dai jam'iyyar shugaban kasar ta APC ta yi martani mai zafi, inda ta kare shi tare da cewa ba a Najeriya kawai ake fama da matsaloli ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng