Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

  • Yan bindigan da suka yi awon gaba da ɗalibai a FGC Birnin Yauri sun saki hotunan waɗanda suka kama
  • A makon da ya gabata ne maharan suka dira makarantar sakandiren, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai
  • Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, yayi alƙawarin kuɓutar da ɗaliban cikin ƙoshin lafiya

Yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar sakandiren gwamnatin tarayya FGC dake Birnin Yauri, jihar Kebbi, sun saki hotuna dake nuna halin da ɗaliban ke ciki, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Ƙasa Kan Yan Boko Haram a Dajin Borno

A makon da ya gabata ne yan bindigan suka kai hari makarantar, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai da malamai guda huɗu.

Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rundunar soji tace ta kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace a wata musayar wuta da suka yi da maharan.

Gwamnan Bagudu ya yi alƙawarin kuɓutar da ɗaliban

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, ya tabbatar wa iyayen ɗaliban da aka sace cewa gwamnatinsa zata dawo musu da yayan su cikin koshin lafiya.

Gwamnan yayi alƙawarin cewa zai haɗe da mafarautan dake taimakawa jami'an tsaro, su shiga daji kuɓutar da yaran, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓutar da Malami da Wasu Dalibai

Wani malami a makarantar FGC wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana sunayen waɗanda ke cikin hotunan da ɓarayin suka saki.

Kalli hotunan a ƙasa

Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani labarin kuma Sojoji Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram Yayin da Suka Kai Hari Sun Hallaka da Dama a Borno

Sojoji sun samu nasarar daƙile harin yan ta'addan Boko Haram a Ƙunmshe, jihar Borno.

Kakakin sojin yace an yi gumurzu sosai tsakanin sojojin da yan ta'addan waɗanda suka zo da motocin yaƙi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel