Mun Biya Fansa Ga ’Yan Bindiga Sama da N2000000000 a Shekara Daya, ’Yan Kaduna

Mun Biya Fansa Ga ’Yan Bindiga Sama da N2000000000 a Shekara Daya, ’Yan Kaduna

  • Kungiyar Al'ummar Kudancin Kaduna ta bayyana irin makudan kudin da ake kashewa wajen biyan fansa
  • Kungiyar ta ce a shekarar da ta gabata kadai an kashe kudin da ya haura sama da N2bn ga 'yan bindiga
  • Kungiyar ta kuma koka kan yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a yankunan kudancin Kaduna

Kungiyar Al'ummar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta ce gamayyar iyalai sun biya sama da N2bn a matsayin kudin fansa ga masu satar mutane a Kudancin Kaduna don sakin wadanda aka yi garkuwa da su daga hannun makiyayan da ke dauke da makamai a shekarar da ta gabata.

Kakakin SOKAPU, Luka Binniyat, ya gabatar da wadannan batutuwan ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Punch a Abuja.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Bayan Shekaru 6, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC

Mun Biya Fansa Ga ’Yan Bindiga Sama da N2000000000 a Shekara Daya, ’Yan Kaduna
Wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewarsa:

“Mun kiyasta cewa a kalla, mutanen Kudancin Kaduna sun biya N2bn a matsayin kudin fansa ga masu satar mutanen don sakin 'yan uwansu da ke hannun masu garkuwar da mutane, makiyaya dauke da makamai a cikin shekara guda da ta gabata.
“A yau, akwai kusan al’umma 108 da ke karkashin mamayar wadannan makiyaya masu dauke da makamai a Kudancin Kaduna. Dubban dubatan mutane sun yi watsi da gonakan sun bar yankin.
“Gaskiyar magana mai ban tsoro ita ce, maharan suna samun karfin gwiwa kuma suna dab da shiga garin Kaduna.
"Misali, Kakau na da nisan kilomita 20 daga Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna. Amma Unguwan Madaki na da nisan kilomita 7 daga gidan Sir Ibrahim Kashim (Gidan Gwamnati) dake Kaduna.”

Lamurran tsaro na kara tabarbarewa a yankin Kudancin jihar Kaduna

Hakazalika, kungiyar ta koka kan yadda lamurran tsaro suka kara lalacewa a yankin na Kudancin kaduna.

Kakakin SOKAPU ya kara da cewa:

“Ranar Juma’ar da ta gabata, da misalin karfe 10 na dare, wasu makiyaya dauke da makamai sun far wa Anguwan Madaki da ke Unguwar Kakau, suka tafi da mutane 26 suka kashe biyu.
"Ranar 22 ga Mayu, 2021, a wani kauye da ake kira Libere, a cikin unguwar Kallah, karamar hukumar Kajuru; duk a Kudancin Kaduna, makiyaya dauke da makamai sun far wa kauyen suka tafi da mutane 77.
“Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, yana ba da rahoto a kullum a kan yanayin tsaro a Jihar Kaduna amma bai taba ambaton wadannan munanan barna da aka yi wa mutanenmu ba."

SOKAPU ta ba mazauna tabbacin dawo musu da gonakansu da Fulani makiyaya suka kwace

Kungiyar ta kuma ba da tabbaci ga wadanda suka rasa filayensu a hannun Fulani makiyaya da ke Kudancin Kaduna cewa za a dawo musu da filayensu ta kowane hali, komai lokacin da za a yi, in ji rahoton jaridar Guardian.

Shugaban SOKAPU, Jonathan Asake, ya ba da tabbacin hakan ne a karshen mako, lokacin da ya ziyarci hakimin kauyen Unguwan Madaki, Na’Allah Na’Dare a yankin Kakau, karamar hukumar Chikun da ke Kudancin Kaduna.

KU KARANTA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa

Hotunan yadda jama'ar Zaria suka yi wa 'yan bindiga sallar Al-Qunuti

A wani labarin daban, Al'ummar Zaria sun gudanar da Sallar Al-Qunut da addu'oi tsawon mako daya domin neman saukin rikicin 'yan bindiga masu satar mutane da suka addabi yankin.

Dr Shamsuddeen Aliyu mai yasin garkuwan makarantar Zazzau daya daga cikin wadanda suka jagoranci Sallar da addu'oin ya shaida wa BBC cewa an gudanar da sallolin ne a filayen Idi da ke cikin kwaryar Zaria.

Ya ce daruruwan mutane ne suka halarci Sallar da zaman addu'oin domin rokon Allah ya yi maganin 'yan bindiga wadanda ya ce sun yi wa garin Zaria kawanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel