Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC Sama da 80

Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC Sama da 80

  • Sojoji sun kashe yan bindiga sama da 80, waɗanda suka sace ɗaliban makarantar FGC Birnin Yauri
  • Shaidu sun bayyana cewa jami'an sojin sun yi amfani da dabarar yaƙi, inda suka yi wa ɓarayin kofar rago
  • A halin yanzu, jami'an sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban

Wasu rahotanni daga jihar Kebbi sun bayyana cewa jami'an rundunar soji sun yi gumurzu da yan bindigan da suka sace dalibai a makarantar gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri, jihar Kebbi, inda suka hallaka aƙalla 80.

KARANTA ANAN: Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani

Wasu shaidu sun tabbatar wa BBC cewa sun ƙirga aƙalla gawar masu garkuwan guda 80, waɗanda sojoji suka hallaka.

Shaidun sun ƙara da cewa an yi musayar wuta sosai tsakanin jami'an rundunar soji da kuma yan bindigan.

Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga Sama da 80
Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC Sama da 80 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa jami'an sojin sun kewaye yan bindigan a daji ranar alhamis da daddare.

"Abin da ya faru a garin Makoko, inda yan bindigan suka mai da daji, jami'an soji sun tare su, aka fafata tsakanin su. Yanzu haka maganar da nake maka an tara gawa sama da mutum 80 na yan bindigan," inji wani shaida.

Ana cigaba da tara gawarwakin yan bindigan a wata firamare dake Makoko, sannan kuma ba'a kashe soja ko ɗaya ba.

KARANTA ANAN: Ba Zan Runtsa Ba Har Sai Dukkan Yan Gudun Hijira Sun Mallaki Mahalli, Shugaba Buhari

Sojoji sun kuɓutar da wasu daga cikin ɗaliban

Rahoton vanguard ya nuna cewa a yayin fafatawar da sojoji suka yi da yan bindigan, sun samu nasarar kuɓutarda wasu ɗalibai tara daga cikin waɗanda aka sace.

Wani shaida ya tabbatar da cewa yaran da aka kuɓutar suna garin Makoko, kuma shugaban ƙaramar hukumar Sakaba ya tura likitoci su dub lafiyar su.

Ɗan majalisa mai wakilar Yawuri a majalisar dokokin Kebbi Honorabul Muhammad Bello Ngaski ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ngaski yace tun bayan sace ɗaliban aka baiwa jami'an tsaro umarnin su tare hanyar Sakaba, inda ake tsammnin ta nan yan bindigan zasu bi.

"A halin yanzun an kubutar da ɗalibai tara daga hannun yan bindigan, kuma suna cikin ƙoshin lafiya," inji shi.

A wani labarin kuma Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno

Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi a akan yan Najeriya biyan bashi ne.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa zata yi iya bakin ƙoƙarinta wajen inganta rayuwar yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel