Matsalar Tsaro: Gwamna Ya Kulle Wasu Makarantu a Jiharsa Saboda Sace Ɗalibai a Birnin Yauri

Matsalar Tsaro: Gwamna Ya Kulle Wasu Makarantu a Jiharsa Saboda Sace Ɗalibai a Birnin Yauri

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta bada umarnin kulle wasu makarantu a jihar guda baƙwai
  • Shugaban ƙungiyar malaman makaranta, NUT, shine ya tabbatar da matakin gwamnatin ga manema labarai
  • Yace an tura jami'an tsaro da yan sa kai makarantun da abun ya shafa don sanya ido da tsaro

Gwamnatin Kebbi ta kulle wasu makarantu bakwai dake jihar biyo bayan sace ɗalibai a makarantar gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri ranar Alhamis, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno

Shugaban ƙungiyar NUT na jihar, Isah Arzika, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa gwamnatin Kebbi ta umarcin shugabannin makarantun sakandire da su kulle duk wata makaranta da suke ganin babu tsaro.

Ya ƙara da cewa an tura jami'an yan sanda da kuma yan bijilanti makarantun domin su sanya ido a kan su kuma su kare su.

Gwamnatin Kebbi ta kulle wasu makarantu
Matsalar Tsaro: Gwamna Ya Kulle Wasu Makarantu a Jiharsa Saboda Sace Ɗalibai a Birnin Yauri Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yace: "Gwamnati ta bamu umarnin mu ɗauki dukkan matakin da ya kamata a kan makarantun jihar, sannan mu kulle duk makarantar da muke ganin akwai barazanar kawo hari musamman waɗanda suke a yankin da babu tsaro."

Shugaban NUT yace an riga da an kulle waɗannan makarantu dake kan gaba a wasu yankuna, kuma wannan mataki ne na kare rayuwar ɗaliban jihar.

KARANTA ANAN: El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

Shugaban NUT yayi magana kan ɗaliban da aka sace a FGC

Shugaban NUT, Arziƙa, yayi kira ga iyayen ɗaliban da aka sace a FGC da su kwantar da hankalinsu, su cigaba da addu'a Allah ya dawo da zaman lafiya a Kebbi da ƙasa baki ɗaya.

Yace: "Tun da jami'an tsaro suka fara aiki kan ɓarayin da duka sace ɗaliban, bamu sake tattaunawa da iyayen yaran ba."

"A maganar da muka yi da su kwana biyu da suka gabata, sun shaida mana cewa ɓarayin ba su nemi kuɗin fansa ba, amma sun tuntuɓi iyayen don su tabbatar musu yayan su na tare da su."

A wani labarin kuma PDP Ta Ragargaji APC a Zaɓen Cike Gurbin da Aka Gudanar a Jihar Kaduna

INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbin da ta gudanar a mazaɓar Tudun Wada, Zaria, jihar Kaduna, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Baturen zaɓen yankin, Dr. Muhammed Musa, ya bayyyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262