Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Dagaci da Matarsa a Ibadan

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Dagaci da Matarsa a Ibadan

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da Dagacin ƙauyen Araro, Chief Tafa Apanpa, tare da matarsa a jihar Oyo
  • Wani mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Talata
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da sace Dagacin, yace jami'ai sun duƙufa bincike

Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun yi awon gaba da Dagacin Auraro, Chief Tafa Apanpa, dake yankin Bakatare a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ranar Talata da daddare, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babu Wata Matsalar Tsaro da Ta Fi Matsalar Yunwa Hatsari, Zulum Ya Koka

Vanguard ta ruwaito wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya bayyana cewa an sace shugaban nasu tare da matarsa da misalin ƙarfe 9:00 na dare.

Yan Bindiga sun sace Dagaci a Ibadan
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Dagaci da Matarsa a Ibadan Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, yace lamarin ya faru da daren ranar Talata, 22 ga watan Yuni a ƙauyen Araro.

"Jami'an yan sanda sun duƙufa kan aikin kuɓutar da waɗanda aka sace, sannan su damƙo waɗanda suka aikata hakan."

KARANTA ANAN: Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace

Leigt.ng hausa ta gano cewa yan bindigan sun kai hari ƙauyen ne lokacin da mutane ke shirin kwantawa bacci, inda suka tafi kai tsaye zuwa gidan dagacin kuma suka sace shi tare da matarsa.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

Yan bindigan da suka yi awon gaba da ɗalibai a FGC Birnin Yauri sun saki hotunan waɗanda suka kama.

A makon da ya gabata ne maharan suka dira makarantar sakandiren, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel