'Yan bindiga sun kira iyayen daliban kwalejin Kebbi, sai dai basu nemi fansa ba

'Yan bindiga sun kira iyayen daliban kwalejin Kebbi, sai dai basu nemi fansa ba

  • Kungiyar malaman makaranta ta bayyana cewa, 'yan bindiga sun nemi iyayen daliban Yauri
  • Kungiyar ta kuma ce, sai dai 'yan bindiga basu nemi kudin fansa ko kobo a hannun iyayen
  • Zuwa yanzu jihar ta rufe makarantu bakwai domin tsoron hare-haren 'yan bindiga a yankin

Rahoto daga jaridar Cable ya bayyana cewa, Isah Arzika, shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Kebbi (NUT), ya ce wadanda suka sace daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, sun tuntubi iyayen yaran.

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun far wa makarantar a ranar Alhamis, kuma suka yi awon gaba da daliban da ba a san yawansu ba bayan arangama da jami'an 'yan sanda dake bakin makarantar, The Gaurdian ta ruwaito.

A baya-bayan na, an kubutar da dalibai biyar da malamai biyu, yayin da dalibi ya mutu a yayin aikin ceto da jami'an tsaro suka yi.

KU KARANTA: Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

'Yan Bindiga Sun Kira Iyayen Daliban Kebbi, Amma Basu Nemi Kudin Fansa Ba
'Yan Bindiga Dauke Makaimai | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake magana da kamfanin dillacin labarai ta Najeriya (NAN), Arzika ya ce masu garkuwar sun tuntubi iyayen dalibai da dangin sauran wadanda aka sace don sanar da su cewa ’ya’yansu suna hannunsu.

A cewarsa, 'yan bindigan ba su nemi kudin fansa ba.

Ya kuma kara da cewa 'yan bindigan ba su sake tuntubar wani mutum ba bayan aikin ceton da jami'an tsaro suka yi.

Arzika ya ce:

"Tun da jami'an tsaro suka fara aiki a kan 'yan bindiga, ba mu sake tuntubar iyaye da dangin dalibai da kuma malaman da ke hannunsu ba.
“Lokacin da suka fara tuntubarmu kwanaki biyu da suka gabata, daidai ranar Alhamis, ba su nemi kudin fansa ba. Madadin haka, sun gaya wa iyayen da dangin cewa kawai suna son kulla hulda da su ne kuma sun sanar da su cewa yaransu suna tare da su.

An rufe makarantu bakwai a jihar Kebbi

Shugaban na NUT ya bayyana cewa:

“Yayin da nake zantawa da ku, daga cikin malamanmu biyu sun dawo. Tuni, makarantu bakwai da ke kan gaba a wannan yankin an rufesu kuma za a rufe wasu idan har mun fahimci cewa lamarin ba aminci ga malamai da daliban ba.
“Akwai sadarwa a wurinsu, amma babu wani daga cikinsu da ya nemi ko kobo. Kawai sun ce suna son su sanar cewa wadanda suka sace din suna hannunsu.

KU KARANTA: Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin artabu da 'yan sanda

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Benue ta tabbatar da cewa 'yan bindiga 14 sun mutu a yayin musayar wuta bayan wani yunkurin kai hari a wani ofishin 'yan sanda a garin Katsina-Ala, jihar Benue da safiyar Lahadi, The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun ‘yan sanda DSP Kate Anene, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce a ranar Asabar, an kama wasu da ake zargin 'yan bindiga ne kuma an tsare su a ofishin ‘yan sanda da ke Katsina-Ala domin gudanar da bincike.

Amma ta ce a safiyar ranar Lahadi, da misalin karfe 1 na dare, wasu ‘yan bindiga, wadanda yawansu ya kai 50, sun kai wani mummunan hari a ofishin 'yan sanda a kokarin su na kubutar da wadanda ake zargin dake tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel