Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mai Horad Da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mai Horad Da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa

  • Yan bindiga sun sace mai horad da tawagar yan wasan kwallon ƙafa ta Rivers United, Stanley Eguma
  • Wata majiya dake kusa da hukumar shirya wasanni ta ƙasa NPFL ta tabbatar da faruwar lamarin
  • Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Rivers United ta sha kashi a hannun takwararta Adamawa United ranar Lahadi

Wasu yan bindiga sun sace mai horad da ƙungiƴar ƙwallon ƙafa ta Rivers United, Stanley Eguma, a kan hanyarsa ta komawa gida daga jihar Gombe bayan ƙungiyarsa ta sha kashi a hannun Adamawa United Ranar Lahadi, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari

Wata majiya dake kusa da hukumar shirya wasannin ƙwallo a Najeriya (NPFL) ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Laraba.

Mai horad da ƙungiyar Rivers United, Stanley Eguma
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mai Horad Da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar majiyar, an sace Eguma ranar Litinin yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Rivers daga Gombe bayan tawagar yan wasan sa sun sha kaye a hannun Adamawa United.

KARANTA ANAN: Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara

Bamu sake ji daga yan wasa ba sai da aka sace Eguma, NPFL

Majiyar tace: "Tun da yan wasan Rivers United suka tafi, bamu sake ji daga gare su ba. Daga baya hukumar mu ta sami labarin an sace Eguma."

"Yan wasan ƙungiyar tare da ma'aikata sun kwana a jihar Enugu, amma basu ga mai horad da ƙungiyar ba da safe."

"A halin yanzun, shugabannin ƙungiyarsa sun fara tattaunawa da masu garkuwan domin samun masalaha."

Hukumar yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da sace mai horad da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta jihar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

A wani labarin kuma Hukumar zaɓe, INEC Ta Bayyana Sabon Adadin Runfunan Zaɓe a Najeriya, Ta Soke Wasu 746

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta soke runfunan zaɓen dake masallatai da Coci-Coci, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya faɗi haka ranar Laraba a babban birnin tarayya, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262