Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓutar da Malami da Wasu Dalibai

Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓutar da Malami da Wasu Dalibai

  • Sojoji sun sake fafatawa da ɓarayin ɗaliban FGC Birnin Yauri, sun kuɓutar da malami da ɗalibai uku
  • Kakakin rundunar sojin ƙasa, Nwachukwu, yace an sake tura ƙarin sojoji yankin domin hana maharan tserewa
  • A baya dai jami'an sojin sun yi wa yan bindigan ƙofar rago, inda suka kashe aƙalla mutum 80 daga cikin su

Rundunar sojin ƙasa ta bayyana cewa jami'anta sun sake kutsawa cikin daji domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace a Birnin Yauri, kuma sun samu nasarar sake kuɓutar da wani malami da ɗalibai 3, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

A yayin wannan operation, Sojoji sun kashe ɗan ta'adda ɗaya tare da kwato mashina 9, waɗanda suke mallakin ɓarayin.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno

Kakakin rundunar soji, Brig. Janar Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana haka, yace an ƙara tura wasu jami'an soji domin tsaftace yankin da kuma hana ɓarayin tserewa.

Sojoji sun ƙara ragargazan yan bindiga
Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓuatar da Malami da Dalibai 3 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yace: "Malami ɗaya da wasu ɗalibai uƙu sun kuɓuta a wani Operation da sojoji suka fita ranar Asabar a Makuku."

"Sojoji sun kashe mutum ɗaya daga cikin ɓarayin, sannan sun kwato mashina 9 da kuma wayoyin hannu guda huɗu."

"Rundunar soji ta ƙara tura jami'ai yankin domin su mamaye dajin kuma su hana ɓarayin tserewa."

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Gwamna Ya Kulle Wasu Makarantu a Jiharsa Saboda Sace Ɗalibai a Birnin Yauri

A baya sojoji sun kuɓutar da ɗalibai 5

Tun a ranar jumu'a da ta gabata, gwarazan jami'an soji suka yi artabu da ɓarayin, inda suka kuɓutarda malamai biyu da ɗalibai 5.

Nwachukwu yace: "Idan zaku iya tunawa, a ranar Jumu'a 18 ga watan Yuni, sojoji sun samu nasarar kuɓutar da malamai 2 da ɗalibai 5 daga hannun yan bindigan."

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya gargaɗi mutanen jihar sa a kan toshe hanyar Kaduna-Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin ziyarar ta'aziyya da yakai yankunan, inda ya tattauna da mutanen yankunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel