Kasashen Duniya
A Ranar Lahadi, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wani nadin sarauta a kasar Turai yayin da ake rade-radin sabon rikici tsakaninsa da Gwamna. A karon farko Mai martaba Sarki Sanusi II ya yi zaman fada a kasar waje.
A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar 17 ga watan Satumba, ta bayyana wasu dalilai da suka sanya ake matsananciyar takun saka da muguwar adawa da juna tsakanin kasar Saudiya da kuma Iran.
Mahukunta a ranar Lahadi sun ce an harbe wani babban bafade na Sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, yayin da mutane 7 suka jikkata da suka hadar da jami'an tsaro biyo bayan wata takaddama ta cacar baki da ta auku a Jedda.
Duk da kullaliyar dangantaka dake tsakanin Najeriya da kasar Saudiyya, amma sai gashi a cikin sunayen da kasar ta fitar na kasashen da za ta dinga bawa mutanensu Visa idan sun isa kasar babu Najeriya a ciki...
Jaridar BBC Hausa ta ruwaito mahukunta a kasar Pakistan sun ce, rayukan mutane 19 sun salwanta a yayin da fiye da mutane 300 suka jikkata a sanadiyar wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki 5.8 da ta auku a Gabashin kasar.
Shekaru biyu bayan karewar wa'adin shugaban kasar Amurka na 44 a tarihi, Barack Obama, wata shahararriyar mai daukansa hotuna, Callie Shell, ta saki wasu zafafan hotunansa da babu lallai idanu sun taba kai wa gare su.
Dangane da sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na zauren sada zumunta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 74 a tarihi.
Tsohon shugaban kasar Tunisia na mulkin kama-karya, Zine El-Abidine Ben Ali ya rigamu gidan gaskiya a kasar Saudiyya inda ya tsere domin neman mafaka tun a shekarar 2011
Hafiz wanda ya kasance haifaffan jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, shi ne ya fito Zakara wajen lashe musabakar karatun Al-Qur'ani ta duniya ta bana da aka gudanar a kasar Saudiya.
Kasashen Duniya
Samu kari