Gwamnati Ta Yi Magana da Yan Bindigan da Suka Sace Mutane a Masallacin Juma'a? Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu masu garkuwa ba su tuntube ta kan mutanen da suka sace a masallacin Juma'a ba
- Wasu rahotanni sun nuna cewa an zargin kungiyar Lakurawa da mayakan Boko Haram ne ke da hannu a harin
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro su gaggauta ceto duka masallatan da ke hannun yan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu ba ta samu wata sanarwa ko tuntuba daga ’yan ta’addan da suka sace masu ibada a wani masallaci da ke karamar hukumar Borgu a ranar Juma’ar da ta gabata ba.
Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago ta ce yan bindigan da suka sace masallatan ba su tuntube ta ba har yanzu.

Source: Twitter
Gwamnatin Neja ta yi karin haske
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Obed Nuhu, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin wata hira da shirin The Morning Brief na Channels Television.
ya ce harin ya faru ne a wurare uku daban-daban a yankin, kuma ana zargin kungiyoyin ’yan ta’adda na Lakurawa da Boko Haram da hannu.
“Ba a tuntube mu ba, ba mu yi wata tattaunawa da su ba, amma ana zargin Lakurawa kamar yadda suke kiran kansu da Boko Haram. Lamarin ya faru ne a wurare uku daban-daban,” in ji shi.
Mutane nawa aka sace a masallaci?
Kwamishinan ya kuma ce gwamnatin jihar Neja ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba a halin yanzu, saboda jami’ai na ci gaba da tattara bayanai kan harin.
Ya ce gwamnati ba za ta yi hasashe kan adadin mutanen da aka sace ba har sai ta samu sahihan bayanai da aka tabbatar.
Bayan harin, Gwamnan Neja, Umaru Bago, ya nuna damuwa kan lamarin tare da umartar hukumomin da abin ya shafa da su hada kai da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Gwamnan ya kuma sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar Neja, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakai domin hana miyagu kawo cikas ga zaman lafiya a fadin jihar.

Source: Original
An kaddamar da aikin ceto
Gwamnatin jihar ta ce an kaddamar da wani aikin hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro a yankin domin tantance halin da ake ciki, bibiyar wadanda suka kai harin da kuma taimakawa wajen kubutar da mutanen da aka sace.
Ta kara da cewa ba za a bayyana cikakkun bayanai kan yadda jami’an tsaro ke zirga-zirga da kuma inda aka jibge su ba saboda yanayin aikin da ake gudanarwa.
Yan sanda sun baza koma a Neja
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a Jihar Neja sun tsaurara matakan da suke dauka domin ceto masallata da yan bindiga suka sace a a Borgu.
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai kula da Zone 7, Victor Olaiya, domin jagorantar aikin ceto wadanda aka sace.
Asali: Legit.ng

