"Ba Irin na Baya ba ne"; Amaechi Ya Fayyace Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Fetur

"Ba Irin na Baya ba ne"; Amaechi Ya Fayyace Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Fetur

  • Chibuike Amaechi ya ce shirin Atiku Abubakar na tallafin man fetur ba zai mayar da Najeriya kan tsohon tsarin tallafin man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje ba
  • Tsohon gwamnan Rivers ya bayyana cewa za a tallafa wa matatun mai na cikin gida domin rage farashin fetur da kuma ƙara wa ‘yan Najeriya ƙarfin sayayya
  • Amaechi ya ce samar da danyen mai mai rahusa ga matatun cikin gida zai taimaka wajen rage farashin fetur, samar da ayyukan yi da rage tsadar sufuri da wutar lantarki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Chibuike Rotimi Amaechi, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), ya yi magana kan shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur.

Amaechi ya ce shirin Atiku Abubakar, na tallafin man fetur ba wai komawa tsohon tsarin tallafin man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ba ne.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Amaechi ya bayyana shirin Atiku kan dawo da tallafi
Abokin takarar Atiku a zaben 2027, Rotimi Amaechi Hoto: Rotimi Amaechi
Source: Twitter

Amaechi, wanda tsohon gwamnan Jihar Rivers ne kuma tsohon ministan sufuri, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 24 ga watan Agustan 2026 yayin taron kungiyar lauyayoyi ta kasa (NBA) da aka gudanar, cewar rahoton TheCable.

Ya ce manufar shirin ita ce tallafa wa samar da man fetur a cikin gida, rage farashin mai da kuma dawo da ƙarfin sayen kayayyaki ga ‘yan Najeriya.

Za a tallafa wa matatun cikin gida

A cewar Amaechi, gwamnatin Atiku za ta mayar da hankali ne wajen samar da yanayin da zai ba matatun mai na cikin gida damar samun danyen mai cikin sauƙi da rahusa.

Ya ce hakan zai bai wa matatun damar tace mai da ƙaramin kuɗi, sannan su sayar da fetur ga ‘yan Najeriya kan farashi mai sauƙi.

“Abin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku yake ba da shawara ba wai ya kauce daga cire tallafin man fetur ba ne. Yana cewa a cikin shekaru huɗu na farko da muka karɓi wannan ofishi, za mu sanya kuɗi a hannun ‘yan Najeriya domin su samu damar sayen wannan fetur,” in ji Amaechi.

Kara karanta wannan

An gano manyan hadurra 3 a shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ga 'yan Najeriya

Ya ƙara da cewa za a yi amfani da tsarin ne wajen ƙarfafa samar da man fetur a cikin gida.

“Yadda za a yi hakan shi ne ta hanyar ƙarfafa samar da mai a cikin gida. Za mu tallafa wa samar da mai a cikin gida ne kawai,” in ji shi.

Amaechi ya ce tsarin zai rage tsadar rayuwa

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa samar da danyen mai cikin rahusa ga matatun cikin gida zai taimaka wajen rage kuɗin tace mai da kuma farashin da masu amfani za su biya.

A cewarsa, hakan zai iya taimakawa wajen ƙara ƙarfin sayen fetur ga jama’a tare da ƙarfafa harkokin tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Amaechi ya kuma danganta tsadar man fetur da ƙarin tsadar wasu muhimman abubuwa kamar wutar lantarki da sufuri.

Amaechi ya yi bayani kan shirin Atiku
Chibuike Rotimi Amaechi tare da Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Facebook
“Za mu samar muku da dukkan abubuwan da ake buƙata domin tallafawa samar da mai a cikin gida kawai, domin ƙarfafa tattalin arziki, wanda zai samar da ayyukan yi,” in ji shi.

Ya ce idan aka samu rahusa wajen samar da man fetur, hakan zai taimaka wajen rage nauyin tsadar makamashi da sufuri da ke addabar ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya saba da Atiku, ya bayyana babbar matsalar dawo da tallafin fetur

An soki Atiku kan shirin dawo da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da shirin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur.

Fadar ta bayyana shirin a matsayin wata manufar tattalin arziki da za ta magance alamomin matsala na dan lokaci, maimakon magance tushen matsalolin da ke addabar bangaren makamashi na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng