INEC Ta Shirya Fadin Sunayen 'Yan Siyasar da za Su Yi Takarar Gwamna a 2027
- Hukumar INEC za ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi a ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026
- Za a gudanar da zaben gwamna a jihohi 28, yayin da za a gudanar da zaben majalisun dokokin jihohi a dukkan jihohi 36 na Najeriya
- Ana sa ran jam'iyyun siyasa su kammala gabatar da sunaye da sauya 'yan takara kafin INEC ta wallafa jerin sunayen 'yan takarar zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta fitar da jerin sunayen 'yan takara da jam'iyyun siyasa suka tsayar domin zaben gwamna da na majalisun dokokin jihohi a ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026.
Ana sa ran za a gudanar da zaben gwamna da na majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027, a matsayin wani bangare na babban zaben kasa da za a gudanar a shekarar.

Source: Twitter
Punch ta rahoto cewa INEC ta bayyana cewa fitar da jerin sunayen zai bai wa jam'iyyun siyasa, 'yan takara da sauran jama'a damar tantance bayanan da aka gabatar mata.
Jihohin da za a yi zaben gwamna
Za a gudanar da zaben gwamna a jihohi 28, ciki har da Lagos, Ogun, Oyo, Delta, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Enugu, Ebonyi da Abia.
Sauran jihohin sun hada da Kwara, Benue, Plateau, Niger, Nasarawa, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto.
Sai dai ba za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Ondo, Osun, Ekiti, Edo, Bayelsa, Anambra, Imo da Kogi ba, sakamakon yadda tsarin gudanar da zabensu ya bambanta da sauran jihohin kasar.
Sabon bayani kan 'yan takarar 2027
Hukumar INEC ta kuma bayyana cewa tana sa ran jam'iyyun siyasa za su gabatar da jerin sunayen karshe na 'yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya kafin ranar Asabar, 29 ga Agusta.
The Nation ta wallafa cewa an riga an ba 'yan takarar da ke son janye kansu daga zaben wa'adin yin hakan kafin ranar 22 ga Agusta, 2026.
A karkashin sashe na 31 na Dokar Zabe ta 2026, dan takarar da ke son janye kansa dole ne ya gabatar da rubutacciyar sanarwa tare da takardar rantsuwa ga jam'iyyar da ta tsayar da shi.

Source: Facebook
Ana sa ran INEC za ta wallafa jerin sunayen karshe na 'yan takarar shugaban kasa da na majalisar dattawa da ta wakilai a ranar 12 ga Satumba, 2026.
Malami ya kafa kwamitin kamfen
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar ADC mai mambobi 600 a jihar Kebbi.
Malami ya bukaci mambobin kwamitin da su rungumi hadin kai, sulhu da kuma siyasar da ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi al'umma gabanin babban zaben 2027.
Ya ce an kafa kwamitin ne domin gina ingantaccen tsarin yakin neman zabe daga tushe, wanda zai taimaka wajen tattara goyon bayan jama'a a kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi.
Asali: Legit.ng

