Matar Aure Ta Biyewa Zuciya Ta Kona Diyar Mijinta da Ruwan Zafi
- An kai Zara Muhammad, wata mai shayarwa, asibiti bayan zargin matar mahaifinta ta kona ta da ruwan zafi a yankin Kofa da ke Maiduguri
- Shaidu sun ce rikicin ya samo asali ne daga gardama tsakanin matan biyu, kafin lamarin ya rikide zuwa mummunan hari da ya jikkata Zara
- Hukumar kula da harkokin mata ta Borno ta shiga tsakani, inda aka kai Zara asibiti domin samun kulawa, yayin da aka kama matar auren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - An kwantar da wata mai shayarwa, Zara Muhammad, a asibiti bayan zargin cewa matar mahaifinta ta kona ta da ruwan zafi a yankin Kofa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026 bayan wata takaddama ta baki tsakanin matan biyu.

Source: Original
Wata maƙwabciya, wadda ita ma aka bayyana sunanta da Zara, ta ce ihun wadda abin ya shafa ne ya sanar da mazauna yankin cewa akwai matsala, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ta ce da ta garzaya gidan, ta tarar da matar gidan tana matsa Zara a kan ruwan zafin da ya zube a ƙasa.
“Na tsawata mata sannan na yi amfani da dukkan ƙarfina wajen raba ta da yarinyar. Abin takaici, ta riga ta samu munanan kuna kafin mu ceci ta,” in ji maƙwabciyar.
Zargin cin zarafi bayan samun ciki
Wasu mazauna yankin sun yi zargin cewa Zara ta fuskanci matsaloli tun bayan da ta samu ciki, bayan mutumin da ta yi hulɗa da shi ya yi watsi da ita.
Sun ce iyayenta sun taɓa matsa mata ta zubar da cikin, amma ta ƙi amincewa da hakan.
Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa bayan ta haifi ɗanta, ana tauye mata abinci tare da cin zarafinta a lokutan da rashin jituwa ya shiga tsakaninta da matar mahaifin nata.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Zara ta bayyana abin da ya faru
Da take bayyana abin da ya faru, Zara Muhammad ta ce matsalar ta fara ne bayan ɗiyarta ƙarama ta yi ƙoƙarin shiga ɗakin matar mahaifinta.
Ta ce matar gidan ta hana yarinyar shiga, lamarin da ya sa ta shiga tsakani domin ta ɗauki ɗiyarta ta tafi.
A cewarta, rashin jituwar ta ci gaba har na tsawon kwanaki uku, kafin matar mahaifin nata ta yi barazanar daina ba su abinci.
“Lokacin da na ce Allah zai azurta ni da ƙaramar ɗiyata, sai ta taso da sauri ta matsa ni cikin ruwan zafin da ta zubar a ƙasa,” in ji Zara.
An kai ta asibiti, an cafke matar gidan
Shaidu sun yi zargin cewa bayan harin, an bar Zara cikin azaba ba tare da samun isasshen kulawar lafiya ba.
Sai dai mahaifin Zara ya musanta zargin cewa an yi sakaci da ita ko kuma ana ƙoƙarin kare matarsa.
“Har an kai ta asibiti,” in ji shi.
Bayan shiga tsakani da Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Borno, Hajiya Zuweira Gambo, wata tawagar agaji ta dauki Zara zuwa wata cibiyar lafiya domin yi mata magani.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun kama matar gidan tare da tsare ta domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi mata.

Source: Facebook
Matar aure ta halla mijinta
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mata mai suna Innocent Serah ta shiga hannun ’yan sanda bayan an zarge ta yin ajalin mijinta, Innocent Nwaoji.
Ana dai zargin matar ta soka wa mijinta, Innocent Nwaọjị, wuka har ya mutu a Umuokereke Ngwa, ƙaramar hukumar Obingwa ta jihar Abia.
Asali: Legit.ng

