Wasu hotunan tsohon shugaban kasa Barack Obama tare da iyalansa da baku taba gani ba
Shekaru biyu bayan karewar wa'adin shugaban kasar Amurka na 44 a tarihi, Barack Obama, wata shahararriyar mai daukansa hotuna, Callie Shell, ta saki wasu zafafan hotunansa da babu lallai idanu sun taba kai wa gare su.
Tarayyar Callie Shell da Obama ta faro ne tun a shekarar 2004 a yayin da yake neman takarar kujerar Sanata kamar yadda tarihi ya tabbatar.
A wani sabon littafi da ta wallafa kamar yadda jaridar Independent ta bayar da tabbaci, Shell ta hikaito rayuwar Obama tare da iyalansa, tun yayin da ya kasance dan majalisa, dan takarar shugaban kasa da kuma bayan ya kasance shugaban kasar Amurka na farko da ya fito daga tsatson bakar fata kuma mai asali a nahiyyar Afirka.
KARANTA KUMA: Za'a rantsar da shugabannin kwamitocin majalisar dattawa a ranar Laraba - Sanata Lawan
Kwararriyar mai daukan hoton ta saki hotunan tsohon shugaban kasa Obama tare da matarsa, Michelle da kuma 'ya'yansa mata biyu; Malia da Sasha.
Ga dai sabbin hotunan da Shell ta sanya a cikin littafinta:
1. Obama yayin wata hira da manema labarai ta hanyar wayar tarho a shekarar 2008
2. Obama yana taya 'ya'yansa wanke-wanke bayan karin kumallon safe a shekarar 2007
3. Obama labe yana sauraron ana gabatar da shi a kafar wani bene a shekarar 2009
4. Obama tare da matarsa Michelle tana karanta jawaban da zai gabatar wa magoya bayansa a shekarar 2008
5. Obama ya tsaya kyam domin yin takun karshe a lokacin da zai fice daga fadar gwamnati a matsayin shugaban kasar Amurka na 44 a tarihi
6. Kallon akwatin talabijin tare da iyalansa gabanin wani taron yakin neman zabe a shekarar 2008
7. Yayin da yake karatun jaridu a wata safiya cikin shekarar 2010
8. Neman suna tare da yi wa kai yakin neman zabe a wani taron shakatawa a shekarar 2008
9. Michelle da sanyin wata safiya yayin da ake gaf da gudanar da zaben fidda gwanin takara a mazabar South Carolina a shekarar 2008
10. Obama yayin wani karin kumallon safiya tare da mataimakinsa, Joe Biden, da kuma iyalansu a shekarar 2008
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng