Taron Kasuwanci: Osinbajo ya tafi kasar Norway a ranar Litinin

Taron Kasuwanci: Osinbajo ya tafi kasar Norway a ranar Litinin

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Litinin ya shilla birnin Osla na kasar Norway domin halartar taron kasuwanci na nahiyyar Afirka da kuma kasashen yankin Arewacin nahiyyar Turai.

Kamar yadda jaridar The Punch ta bayar da shaida, wannan sanarwa na kunshe cikin wani sako da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Bayan halartar taron tattalin arziki na musamman wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Litinin, mataimakin shugaban kasar ya kama hanyar birnin Oslo kai tsaye domin wakiltar Najeriya a taron kasuwanci da zai gudana a makon da muke ciki.

Legit.ng ta fahimci cewa, mataimakin shugaban kasar zai halarci taron ne da manufar janyo ra'ayi tare da kwadaitar da masu saka hannun jari na kasashen waje a kan harkokin kasuwancin kasar nan.

KARANTA KUMA: Tinubu zai dora a kan tubalin Buhari idan ya zama shugaban kasa a 2023 - Razaq

A wani rahoto da jaridar ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya ce yadda babba zaben kasa na 2019 ya gudana salin-alin cikin zaman lafiya da aminci, wata babbar alama ce da ke haskaka irin ci gaban da dimokuradiyya ke yi a kasar.

Shugaban kasar ya yi furucin hakan ne a ranar Litinin cikin birnin Abuja yayin bude taron tattalin arzikin Najeriya karo na 25 mai lakanin "Nigeria 2050: Shifting Gears".

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng