Iran Ta Yi Sabuwar Yarjejeniyar Nukiliya da Rasha, Putin zai Gana da Pezeshkian

Iran Ta Yi Sabuwar Yarjejeniyar Nukiliya da Rasha, Putin zai Gana da Pezeshkian

  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, na shirin ganawa a mako mai zuwa
  • Jakadan Iran a Rasha ya ce ganawar za ta gudana ne a yayin taron ƙungiyar SCO da za a yi a Kyrgyzstan
  • Ganawar na zuwa ne bayan Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyar gina sabbin tashoshin makamashin nukiliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bishkek – Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, na iya gana wa a mako mai zuwa yayin da ƙasashen biyu ke ƙara zurfafa haɗin gwiwarsu musamman a fannin makamashin nukiliya.

Rahotanni sun nuna cewa jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya ce shugabannin biyu za su gana ne a yayin taron ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO) da za a gudanar a Kyrgyzstan.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Masoud Pezeshkian da Vladimir Putin
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a hagu da Vladimir Putin a dama
Source: Getty Images

Rahoton Roya News ya nuna cewa hakan na zuwa ne bayan Amurka ta dauki wani mataki domin hana Iran hulda da kasashen duniya da dama.

Batun nukiliyar Iran da Rasha

Ganawar Pezeshkian da Putin na zuwa ne jim kaɗan bayan Iran da Rasha sun cimma wata muhimmiyar yarjejeniya kan gina sababbin tashoshin makamashin nukiliya.

Jalali ya bayyana cewa Tehran da Moscow sun amince da yarjejeniyar fahimtar juna da darajarta ta kai dala biliyan 25 domin gina sababbin cibiyoyin nukiliya.

First Post ta rahoto ya ƙara da cewa an riga an ware fili kusa da Tekun Fasha domin gina ɗaya daga cikin tashoshin da aka shirya ginawa.

A cewar jami'in, wannan yarjejeniya ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar nukiliya tsakanin Iran da Rasha, a daidai lokacin da Tehran ke fuskantar ƙarin matsin lamba da takun-saka da Amurka da ƙawayenta.

Jalali ya kuma jaddada cewa yarjejeniyar Iran da Rasha ba ta da alaƙa da wata yarjejeniyar fahimtar juna da Iran ta rattabawa hannu da Amurka a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur

Pezeshkian da Putin za su tattauna?

Ana sa ran ganawar shugabannin biyu za ta ba su damar tattauna dangantakar Iran da Rasha, da kuma batutuwan yanki da na ƙasa da ƙasa.

Taron SCO da za a gudanar a Bishkek zai haɗa shugabannin ƙasashe mambobin ƙungiyar, ciki har da China, Rasha, India, Iran da Pakistan.

Ƙungiyar SCO na zama wani dandali da ƙasashe mambobinta ke tattauna batutuwan tsaron yankuna, siyasa, kasuwanci da haɗin gwiwar tattalin arziki.

Firaministan kasar Rasha
Vladimir Putin a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A halin yanzu ƙungiyar tana da mambobi 10, waɗanda suka haɗa da China, Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, Uzbekistan, India, Pakistan, Belarus da Iran.

Amurka ta sa wa Iran takunkumi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Amurka ta ƙaddamar da wani sabon kamfen na matsin tattalin arziki kan Iran, inda Ministan Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce ana kai wa hanyoyin samun kuɗin Iran hari a faɗin duniya.

Bessent ya ce takunkuman za su shafi kadarori da ke da alaka da fasaha, zinare, harkokin jiragen sama da sufuri, tare da gargadin cewa ƙasashen da za su ci gaba da hulɗar kuɗi da Iran za su iya fuskantar barazana.

Sai dai Ministan Tattalin Arzikin Iran, Ali Madanizadeh, ya yi watsi da matakin, yana mai cewa wannan “tsohuwar magana ce” kuma Tehran a shirye take ta fuskanci kowane irin yanayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng