Sunaye: Kasar Saudiyya ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da za ta dinga bawa VISA
Duk da kullaliyar dangantaka dake tsakanin Najeriya da kasar Saudiyya, amma sai gashi a cikin sunayen da kasar ta fitar na kasashen da za ta dinga bawa mutanensu Visa idan sun isa kasar babu Najeriya a ciki
An ruwaito cewa kasar ta saki sunayen kasashen ne a jiya Juma'a 27 ga watan Satumbar nan, kwana hudu kenan bayan jakadan kasar Saudiyyar Adnan Mahmoud yayi magana akan cewar a shirye Saudiyya take da ta kara dankon zumunta da Najeriya.
Da yake sanar da sunayen kasashen guda 49, jakadan ya bayyana cewa masu yawan bude idon suna iya zama a kasar Saudiyyar ne na watanni uku kawai.
Haka kuma Najeriya da sauran kasashen da babu sunayen su a ciki, suna iya zuwa ofishin jakadancin kasar su nemi Visa a can.
KU KARANTA: Tashin hankali: Miji ya kone matarshi kurmus akan rikicin sayar da fili
Ga sunayen kasashen da zasu more da wannan garabasa ta karbar Visa idan sun shiga kasar ta Saudiyya:
1. USA
2. Canada
3. Kazakhstan
4. Singapore
5. Brunei
6. New Zealand
7. South Korea
8. Japan
9. Spain
10. Belgium
11. Malaysia
12. Austria
13. Cyprus
14. UK
15. Croatia
16. Estonia
17. Andorra
18. Denmark
19. Germany
20. Bulgaria
21. France
22. Hungary
23. Czech Republic
24. Holland
25. Italy
26. Finland
27. Ireland
28. Lithuania
29. Greece
30. Liechtenstein
31. Monaco
32. Iceland
33. Malta
34. Poland
35. Latvia
36. Norway
37. Russia
38. Luxembourg
39. Romania
40. Slovenia
41. Montenegro
42. Slovakia
43. Switzerland
44. Portugal
45. Sweden
46. Australia
47. San Marino
48. Ukraine
49. China
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng