Neja: Bayan Umarnin Tinubu, an Gano Abin Da Yan Sanda Ke Yi don Ceto Masallatan da aka Sace
- Rundunar ’yan sanda ta tura Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai kula da Zone 7, Victor Olaiya, zuwa jihar Neja
- Hukumar tsaro ta ce tana nazarin bayanan sirri tare da tsara dabarun da za su taimaka wajen gudanar da aikin ceto cikin nasara
- An yi garkuwa da masallata ne bayan sallar Juma’a a garin Dekara da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger –Rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a Jihar Neja sun tsaurara matakan da suke dauka domin ceto masallata da yan bindiga suka sace a a Borgu.
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai kula da Zone 7, Victor Olaiya, domin jagorantar aikin ceto wadanda aka sace.

Source: Twitter
Channels TV ta kawo labarin cewa aikin na gudana ne tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, da nufin ganin an kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su cikin aminci.
Za a ceto masallata a jihar Neja
A ruwayar Premium Times, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Elleman, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis 27 ga watan Agusta, 2026 yayin wata ganawa da manema labarai a Minna.
Elleman, wanda jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya wakilta, ya ce za a fara gudanar da aikin ceto yadda ya kamata bisa umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda.
Ya ce a halin yanzu hukumomin tsaro na nazarin bayanan sirrin da suke da su tare da tsara dabarun da za su tabbatar da gudanar da aikin cikin inganci ba tare da wata tangarda ba.
An nemi hadin kan mutanen Neja
A cewarsa, Sufeto Janar na ’Yan Sandan ya kuma samar da karin tallafin aiki, ciki har da tura jami’an Sashen Yaki da Ta’addanci da na Sashen Kula da Ababen Fashewa, domin karfafa aikin ceto.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Maurice Magaji, ya ce gwamnati za ta ci gaba da bada goyon bayan da jami'an bukata domin yaki da rashin tsaro.

Source: Original
Magaji ya nuna damuwa kan kokarin da wasu mutane ke yi na mayar da matsalar tsaron da ke addabar Neja da sauran sassan Najeriya ta siyasa.
Ya bukaci al’umma da su kara hadin gwiwa da jami’an tsaro tare da sanar da su sahihan bayanan da za su taimaka wajen yaki da ta’addanci da sauran laifuka a yankunansu.
Kwamishinan ya ce gwamnati na sane da bukatun jin kai da matsalar rashin tsaro ke haifarwa, yana mai tabbatar da cewa jami’an tsaro za su kula da halin da ake ciki yadda ya dace.
Tinubu ya bada umarni kan masallatan Neja
A wani labarin, kun ki cewa Tinubu ya umarci Sojoji, ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su ceto masallata da aka sace a Neja.
'Yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kutsa masallatai huɗu yayin sallar Juma’a tare da tafiya da masu ibada zuwa daji
Shgaban ƙasa Tinubu ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai an dawo da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su lafiya.
Asali: Legit.ng

