Zabe Ya Gabato amma NDC ba Ta da ‘Dan Takarar Gwamna a Jihar Kaduna
- Shugaban jam'iyyar NDC na jihar Kaduna, Mordecai Ibrahim, ya janye takararsa ta gwamna a hukumance
- Hakan ya sa jam'iyyar ta karyata cewa Danjuma La'ah ko Mohammed Abbas sun riga sun lashe tikitin takarar
- NDC za ta shirya sabon zaben fitar da gwani domin fitar da halattaccen dan takara na gaskiya Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Jam’iyyar NDC mai adawa ta ce har yanzu ba ta tsaida ‘dan takarar gwamna a jihar Kaduna ba duk da ikirarin da wasu ke yi.
Ana rigima tsakanin Sanata Danjuma La’ah da Mohammed Abbas, kowa yana cewa shi ne yake rike da tutar NDC a zaben gwamna na 2027.

Source: Getty Images
Shugaban NDC a Kaduna ya yi karin haske
Shugaban NDC na reshen Kaduna, Evangelist Mordecai Ibrahim, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da Channels ta rahoto.
Mordecai Ibrahim ya fada wa duniya cewa har zuwa yanzu ba su iya shawo kan rigimar takarar gwamna da ake yi a reshen Kaduna ba.
Shugaban jam’iyyar ya ce dole su sake wani zaben tsaida gwani domin su canza ‘dan takarar NDC saboda shi ya hakura da neman gwamnan.
NDC tana da 'dan takarar gwamna a Kaduna?
Evangelist Mordecai Ibrahim ya ce:
"Maganar gaskiya ita ce a mataki na kasa da jiha, a ba a tsaida wane ne ‘dan takarar gwamna a jihar Kaduna ba
"Ko Barrister Mohammed Sani Abbas ko Sanata Danjuma Tellah La’ah ne, ba a dauki wannan mataki ba."
'Dan takara ya hakura da neman zama gwamna
Punch ta rahoto Shugaban jam’iyyar na Kaduna ya ce da farko shi ne ‘dan takarar gwamna a NDC, amma ya janye don radin kan shi.
Bayan ya janye, ya sanar da hukumar zabe ta INEC, kuma ya aika takarda zuwa ga shugaban NDC na kasa kamar yadda doka ta tanada.
A ranar 7 ga Agustan 2026 ya sanar da NDC ta kasa cewa ya watsar da takarar da ya yi niyya.

Source: Getty Images
NDC ba ta tsaida La'ah ko Abbas ba
Shugaban NDC na Arewa, Alhaji Sidi Bomi ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Sanata La’ah ne zai yi wa jam’iyyar takarar gwamna.
Haka kuma Alhaji Sidi Bomi ya ce ba Abbas ba ne wanda NDC ta ba tutar gwamnan Kaduna.
Abin da ya tabbata dai shi ne an samu karin wadanda suka janye daga neman takara a NDC a jihar - Zariyi Madaki Ibrahim Abdulkarim.
Da aka yi wani zama da su, sun goyi bayan tsohon sanatan Kaduna ta Kudu ya samu tikiti.
Mai neman takara ya yi karar NDC a kotu
An samu rahoto cewa Pratt Tunde ya shigar da karar INEC da jam’iyyar NDC a kotun tarayya kan cire sunansa a matsayin dan takarar majalisa.

Kara karanta wannan
Duk da alkawarin da ya yi, NDC ta nemi Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027
Yayin da shugabancin jam'iyyar APC ke yakin neman zabe, NDC ta tsinci kanta a rikicin shari'a sakamakon sauya sunan dan takararta a Legas
Tunde ne ya shigar da karar gaban kotun tarayya domin kare hakkinsa na zama halastaccen dan takara da neman dakatar da sauyin da aka yi.
Asali: Legit.ng

