Taron Majalisar Dinkin Duniya: Buhari ya isa kasar Amurka
Dangane da sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na zauren sada zumunta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 74 a tarihi.
Buhari wanda ya kama hanyarsa a jiya Lahadi, 22 ga watan Satumba, zai kasance shugaban kasa na biyar da zai gabatar da jawabai a yayin babban taron da za a gudanar a Amurka.
Kamar yadda ministan harkokin wajen Najeriya ya sanar, shugaba Buhari zai ribaci wannan taro wajen zayyana wa duniya kudirirrikan da ya yiwa kasar nan tanadi.
KARANTA KUMA: Tsawa ta hallaka shanu 36 a jihar Ondo
Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, ana ganin cewa wannan taron na da matukar muhimmanci ga Najeriya sanadiyar yadda aka nada dan kasar, Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin shugaban babban zauren majalisar dinkin duniya a yanzu.
Taron majalisar dinkin duniya a wannan karo zai tattauna kan maudu'in "Fargar da kasashe wajen yaki da talauci da samar da ingantaccen ilimi da kuma daukar matakai kan sauyin yanayi."
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng