Da dumi dumi: Tsohon shugaban kasar Tunisia ya rasu a kasar Saudiyya

Da dumi dumi: Tsohon shugaban kasar Tunisia ya rasu a kasar Saudiyya

Tsohon shugaban kasar Tunisia na mulkin kama-karya, Zine El-Abidine Ben Ali ya rigamu gidan gaskiya a kasar Saudiyya inda ya tsere domin neman mafaka tun a shekarar 2011, kamar yadda jaridar Aljazeera ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ben Ali ya rasu ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba yana dan shekara 83 bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita a wani babban asibiti dake kasar Saudiyya.

KU KARANTA: Sojoji sun yi alwashin gamawa da Boko Haram idan suka shiga garin Maiduguri

Lauyansa, Mounir Ben Salha ya tabbatar da mutuwar Maigidan nasa, inda yace: “Yanzun nan Ben Ali ya rasu a kasar Saudi Arabia.” Haka zalika shima ministan harkokin kasashen wajen Tunisia ya tabbatar da mutuwar Ali.

A watan Janairu na shekarar 2011 ne Ben Ali ya arce daga Tunisia biyo bayan wata babbar zanga zanga da al’ummar kasar suka gudanar suna bukatar ya sauka daga mulki bayan kwashe shekaru 23 yana mulkin kasar, mulkin zalunci, mulkin mallaka kuma mulkin kama karya.

Wannan zanga zanga ta faru ne bayan wani karamin dan kasuwa Sidi Bouzid ya banka ma kansa wuta ya kashe kansa sakamakon bacin rai daya dameshi bayan jami’an tsaro sun kwace masa dan baron da yake kasa kayansa a ciki yana sayarwa.

Ko a ranar lahadin da ta gabata sai da aka gudanar da zaben shugaban kasa a karkashin tsarin dimukradiyya a kasar Tunisia, inda daga cikin wadanda suka tsaya takarar akwai wani dan gani kashenin Ben Ali, Abir Moussi, wanda ya samu kashi 4 na kuri’un da aka kada.

A shekarar 1987 Ben Ali ya kwace mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Habib Bourguiba wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa na dindindin, watau shugaban kasa na mutu ka raba, amma Ben Ali ya kawar da shi bayan ya bayyana ma duniya cewa Habib ba shi da lafiya.

Masana sun tabbatar da cewa duk da zaluncin da ake zargin Ben Ali da shi a zamaninsa, amma an samu gagarumar cigaban tattalin arziki a kasar, wanda hakan yasa wasu yan kasar suke ta kukan ya dawo bayan an hambarar da gwamnatinsa sakamakon halin matsin tattalin arziki da suka tsinci kansu a ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng