Girgizar kasa ta hallaka mutane 19 a Pakistan
Jaridar BBC Hausa ta ruwaito mahukunta a kasar Pakistan sun ce, rayukan mutane 19 sun salwanta a yayin da fiye da mutane 300 suka jikkata a sanadiyar wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki 5.8 da ta auku a Gabashin kasar.
A yayin da kawo wa yanzu ba a san girman ta'adin da girgizar kasar ta yi ba, maruwaita sun ce ta auku ne daura da birnin Mirpur a yankin Kashmir wanda ke karkashin ikon gwamnatin Pakistan.
Legit.ng ta fahimci cewa, an yi ta yada hotuna a shafin zaurukan sada zumunta dangane da yadda girgizar kasar ta sanya wasu titinunan kasar suka rufta tare da zagwanyewar gidaje.
A yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP mai tushe a Faransa, wani jami'in nazarin yanayi da kuma halayyar kasa na Pakistan, Muhammad Riaz, ya ce girgizar kasar da ta auku ta kai zurfin kilomita 10, kuma barnar da tayi a birnin Mirpur ya fi muni.
KARANTA KUMA: Kudin kamfe na N90bn: Jaridar Vanguard ta nemi gafarar Osinbajo
Bayan girgizar kasar da ta afku a ranar Talata, an ji motsin kasa a wasu wuraren masu nisa da wajen kamar manyan biranen Pakistan da Indiya wato Islamabad da kuma Delhi.
A sanadiyar girgizar kasar da ta auku cikin Pakistan a ranar Talata, an ji alamar motsin kasa a wasu yankuna na nesa kamar biranen Islamabad da New Delhi.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng