Hafiz Idris daga jihar Borno ya lashe musabakar Al-Qur'ani ta duniya a Saudiya

Hafiz Idris daga jihar Borno ya lashe musabakar Al-Qur'ani ta duniya a Saudiya

Wani matashi dan jihar Borno, Hafiz Idris, ya shiga cikin jerin sahun 'yan Najeriya na musamman da suka yi fintinkau a fagen lashe gasar kasa-da-kasa ta duniya.

Matashin ya wakilci Najeriya a yayin gasar karatun Al'Qur'ani ta Sarki Malik Durban da aka gudanar a birnin Makkah.

Hafiz wanda ya kasance haifaffan jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, shi ne ya fito Zakara wajen lashe musabakar karatun Al-Qur'ani ta duniya ta bana da aka gudanar a kasar Saudiya.

KARANTA KUMA: Mama Taraba ta sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Ana iya tuna cewa, hazikai 13 ne daga kasashen duniya daban-daban suka samu manyan kyaututtuka na musamman a yayin gasar hadda, karatu da kuma tajwidin Al-Qur'ani karo na 40 da aka gudanar cikin birnin aminci na Madinah a bara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel