GITEX: Pantami ya kwadaitar da masu zuba hannu jari a kan ribar da ke Najeriya

GITEX: Pantami ya kwadaitar da masu zuba hannu jari a kan ribar da ke Najeriya

Ministan sadarwa na Najeriya, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, a ranar Larabar da ta gabata ya kwadaitar da 'yan kasuwa na duniya da su zuba hannun jari a Najeriya tun a yanzu ko kuma su yi da na sani a lokaci na gaba.

Ministan kasar ya ankarar da 'yan kasuwa na duniya a kan irin moriyar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi tanadi a yanzu a kasar domin samun riba mai girman gaske ta fuskar habakar tattalin arziki.

Furucin ministan ya zo ne a yayin halartar taron hannun jari na nahiyyar Afirka, a wani bangare na daban da taron baja kolin fasahar zamani na GITEX da ke wakana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE.

A na iya tuna cewa a karshen makon da ya gabat ne, Sheikh Pantami ya jagoranci tawagar wakilan Najeriya wajen halartar taron tattauna muhimmancin fasahar sadarwa ta 5G a shirin baja kolin kayan fasahar zamani ta GITEX dake gudana a birnin Dubai.

KARANTA KUMA: Na so Ronaldo ya ci gaba da zama a Real Madrid - Messi

Daga cikin 'yan tawagar ministan sun hadar da shugaban hukumar NITDA, Kashifu Abdullahi; shugaban kwamitin sadarwa na majalisar dattawa, AbdulFatai Buhari; dan majalisar wakilai, Lado Suleja, da sauransu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel