Mutune 4 sun dulmiye a ruwa wajen daukar hoto na 'selfie a Indiya

Mutune 4 sun dulmiye a ruwa wajen daukar hoto na 'selfie a Indiya

A wani rahoto mai ban al'ajabi da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, mun samu cewa wata sabuwar amarya da 'yan uwanta uku sun dilmiye a wata madatsar ruwa yayin da suke yunkurin daukar hoton irin na zamani wato 'selfie'.

Hukumar 'yan sandan Indiya, ita ce ta bayar da shaidar wannan mummunan lamari da ya auku a ranar Lahadi cikin jihar Tamil Nadu da ke Kudancin kasar.

Wadanda suka riga mu gidan gaskiya na cikin wasu mutune shida da suka rike hannu suka shiga cikin ruwan da bai wuce iyaka kungunsu ba a wata madatsar ruwan Pambar, inda tsautsayi ya sanya santsin ya debi daya daga cikin su kuma ya fizgi sauran suka antaya cikin ruwan kuma suka dilmiye.

An tattaro cewa, angon amaryar ya yi nasarar ceto wata 'yar uwarsa amma kaddara ta rigayi fata a kan sauran da suka nutse da ya zuwa yanzu babu amo ballantana labarinsu.

Daga bisani hukumar 'yan sandan ta ce gwanayen ninkaya sun lalubo gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya inda kai tsaye bincike zai ci gaba da gudana.

KARANTA KUMA: Malamai 3 na jihar Legas sun cinye kyautar shugaban kasa ta kwazon aiki

An yi kiyasin cewa Indiya ce kasar da ke kan sahu na gaba a duniya ta fuskar mafi yawan mutanen da mutuwa ta riska yayin daukar hoto na 'selfie'.

Kamar yadda jaridar ta BBC Hausa ta wassafa, wani rahoton dakin adana littafan lafiya na Amurka, kasar Indiya ce mai babban kaso na rabin adadin mutane 259 da aka san da mutuwarsu yayin daukar hoto na 'selfie' a tsakanin shekarar 2011 da 2017. Daga ita kuma sai Rasha da kuma kasar Amurka da Pakistan da suka biyo baya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel