Abin da yasa ake takun saka tsakanin Saudiya da Iran

Abin da yasa ake takun saka tsakanin Saudiya da Iran

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar 17 ga watan Satumba, ta bayyana wasu dalilai da suka sanya ake matsananciyar takun saka da muguwar adawa da juna tsakanin kasar Saudiya da kuma Iran.

Babu shakka kasar Saudiya da Iran wanda suka kasance makotan juna, sun ci gaba da tafka bakin gumurzu a tsakanin su dangane da kasar da ta fi rinjaye wajen mamaye wasu yankuna na daular Larabawa.

An dai shafe tsawon shekaru aru-aru ana adawa da juna a tsakanin kasashen biyu dangane da bambantar ra'ayi da akida ta addini.

Ko wane daya daga cikin kasashen biyu ya rike manyan rassan akidar addinin Islama guda, a yayin da kasar Iran ta kasance mafiya rinjayen al'ummar kasar suka kasance musulmai 'yan akidar shi'a, kasar Saudiya kuma tana yi wa kanta lakabi da jagorar addinin Islama mai akidar Sunna.

A yayin da aka samu wannan rabuwar kai ta bambancin akidar addinin Islama a daular Larabawa ta Tsakiya, da yawa da cikin kasashen yankin sun rabu kashi-kashi wajen bayyana goyon baya a tsakanin kasashen biyu ta fuskar riko a matsayin tafarki na shiriya.

Tarihi dai ya tabbatar da cewa, kasar Saudiya wadda ta kasance mabubbuga kuma tushen addinin Islama, ta dauki kanta a matsayin tambari kuma jagora ta addinin Musulunci.

Sai dai tun a shekarar 1979 kasar Iran ta daura damarar kalubalantar wannan kambu da kasar Saudiya ta rika wanda kimanin tsawon shekaru 15 da suka gabata kawowa yanzu, ake ci gaba da takun saka da kuma mummunar gaba a tsakanin kasashen biyu.

A halin yanzu dai kasashen biyu na ci gaba da fafutikar shimfida tasiran su a wasu kasashen daular Larabawa ta Tsakiya kamar Syria, Bahrain da kuma Yemen.

KARANTA KUMA: NCC ta datse sadarwar layukan waya miliyan 2 a Najeriya

Ana iya tuna cewa, a shekarar 2003 ne kasar Amurka ta kifar da tsohon shugaban kasar Iraqi kuma jagoran masu gwagwarmayar kafa Sunna a kasar Iran ta hanyar amfani da karfin mulki, Saddam Hussein, wanda yayin rayuwarsa bai gushe ba wajen gaba ga akidun shi'a na kasar Iran.

Wannan kutse da Amurka tayi ya bai wa kasar Iran damar ci gaba da habaka akidar shi'a har zuwa yankin Bagadaza da ya zuwa ta ke ci gaba da samun nasara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng