Najeriya da Saudiyya Sun Zauna, An Jaddada Yarjejeniyar game da Matsalolin Tsaro

Najeriya da Saudiyya Sun Zauna, An Jaddada Yarjejeniyar game da Matsalolin Tsaro

  • Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Oluyede, ya ce akwai bukatar faɗaɗa haɗin gwiwar domin ƙara ƙwarewar sojojin Najeriya
  • Ya bayyana haka ne bayan kasar nan da Saudiyya sun amince a kan sabuwar kawancen tsaro da zai taimaka wajen kakkaba matsalar tsaro a Najeriya
  • Jakadan Saudiyya ya bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa a Afrika, tare da jaddada shirye-shiryen ƙasarsa na ƙara tallafa wa Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hedikwatar Tsaron Najeriya ta karɓi bakuncin Jakadan Masarautar Saudiyya a Najeriya, Mai Girma Yousef bin Mohammed Al-Balawi.

An tarbe shi a yayin da ya kai ziyarar ban-girma da nufin ƙara ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shirin Atiku na dawo da tallafin mai na iya tsorata wasu yan ƙasashen waje

Saudiyya ta ziyarci Najeriya
Yariman Saudiyya ya yabawa manufofin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Hedkwatar tsaro ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana ziyarar da cewa za ta zurfafa alaƙar soji da soji, tare da duba wasu sabbin hanyoyin haɗin gwiwa da za su amfani Najeriya da Saudiyya.

Jakadan Saudiyya ya ziyarci hedkwatar tsaro

A yayin ganawar, Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar OO Oluyede, ya tarbi jakadan tare da nuna godiya kan ziyarar. Ya bayyana cewa Najeriya tana bai wa dangantakarta da Masarautar Saudiyya muhimmanci.

Janar Oluyede ya kuma jaddada bukatar ci gaba da bunƙasa hanyoyin haɗin gwiwar da ake da su, musamman waɗanda za su taimaka wajen inganta ƙwarewar jami’an soji da kuma ƙarfin gudanar da ayyukan rundunonin sojin Najeriya.

Ya ce ƙara ƙarfafa irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen inganta ƙwarewar ƙwararru da kuma ingancin ayyukan rundunar wajen tunkarar matsalolin tsaro.

Saudiyya ta tabbatar da goyon baya ga Najeriya

Da yake jawabi, Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, ya bayyana sha’awar ƙasarsa na ƙara ƙarfafa dangantaka da Najeriya, yana mai bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Jakadan Saudiyya ta kai ziyara kan Hafsan hafsoshin tsaron Najeriya
Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar OO Oluyede Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Jakadan ya ce:

“Muna son ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin Saudiyya da Najeriya, domin Najeriya muhimmiyar abokiyar hulɗa ce a Afirka.”

Ya kuma sake tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya a shirye take ta tallafa wajen ƙara kusantar juna da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, musamman a ɓangarorin tsaro da harkokin soji.

A cewar sa, ƙarfafa alaƙar hukumomi da ƙwararru tsakanin rundunonin sojin Najeriya da Saudiyya zai taimaka wajen inganta haɗin gwiwa wajen tunkarar matsalolin tsaron da ƙasashen biyu ke fuskanta.

Saudiyya ta zauna da Najeriya, kasashe 74

A baya, mun kawo labarin cewa Saudiyya ta fara taron shirye-shiryen Hajjin 2027 da ofisoshin kula da aikin Hajji na kasashe sama da 75, ciki har da Najeriya.

Saudiyya ta sanya 26 ga Satumba 2026 a matsayin wa'adin karshe da kasashe za su kammala rajistar maniyyatan Hajjin 2027, inda aka fara shiri da wuri.

Ana sa ran fara isowar maniyyata Saudiyya daga 8 ga Afrilu 2027, yayin da aikin Hajjin zai fara 14 ga Mayu, idan an ga wata a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng