An kashe dogarin sarkin Saudiya a Jeddah

An kashe dogarin sarkin Saudiya a Jeddah

Mahukunta a ranar Lahadi sun ce an harbe wani babban dogari na Sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, yayin da mutane 7 suka jikkata da suka hadar da jami'an tsaro biyo bayan wata takaddama ta cacar baki da ta auku a birnin Jeddah.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SPA (Saudi Press Agency) ya ruwaito cewa, Manjo Janar Abdulaziz al-Fagham, wanda aka saba gani a koda yaushe a matsayin babban dogarin Sarki Salman, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar a Yamma da birnin Jeddah.

Kafofin watsa labarai da dama na duniya sun ruwaito cewa, Manjo Janar al-Fagham ya yi gamo da ajali a yayin da ya kai ziyara wani gidan wanda amininsa, Mamdouh bin Meshaal Al Ali shi ma ya ziyarta a birnin Jeddah, inda zafin cacar baki ta sanya amininsa ya hau dokin zuciya da ta kai ga yin amfani da makami na bindiga.

Mamdouh bayan harbin al-Fagham wanda ajali ya katse masa hanzari a gadon asibiti, ya kuma raunata wani hadimi da dan uwan mamallakin gidan da suka ziyarta.

Gidan talabijin na Al-Ekhbariya ya ruwaito cewa, wannan mummunan lamari ya biyo bayan wata mummunar jayayya da ta auku a tsakanin aminan junan biyu.

KARANTA KUMA: Lokuta 6 da Buhari ya ki yiwa umarnin kotu da'a

Hakazalika Legit.ng ta fahimci, Mamdouh ya bi sahun amininsa inda shi ma ya ce ga garin ku nan a sakamakon rashin mika kai wadda ta sanya aka yi musayar wuta tsakanin sa da hukumomin tsaro, lamarin da ya janyo jikkatar jami'ai biyar.

Mazauna kasar Saudiya sun yi alhinin mutuwar al-Fagham inda da dama suka bayyana ta'aziyyarsu a zaurukan sada zumunta wajen watsa hotunsa a bakin aiki tare da Sarki Salman.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng