Kowa ya debo da zafi bakinsa: Za’a kashe yan Najeriya 119 a kasar Malaysia

Kowa ya debo da zafi bakinsa: Za’a kashe yan Najeriya 119 a kasar Malaysia

Kungiyar Amnesty International dake yakin kare hakkin bil adama a duniya ta bankado wasu jerin yan Najeriya guda 119 da suke zaman jiran mutuwa a kasar Malaysia dake yankin Asia, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan Najeriyan su 119 na daga cikin mutane 1,281 da gwamnatin kasar Malaysia ta yanke ma hukuncin kisa sakamakon aikata laifuka daban daban a fadin kasar.

KU KARANTA: Tsige Maja Sirdin Sarki ta janyo cece kuce da nuna ma juna yatsa a fadar Sarkin Kano

A cikin rahoton data fitar, AI, ta bayyana bukatar a tsawatar ma kasar Malaysia ta daina kashe masu laifi, bugu da kari ta nemi kasar Malaysia ya warware dokar da ta bata daman kashe duk wani mutumi da aka kama da aikata munana miyagun laifuka.

Rahoton ya kara da cewa mutanen dake jiran a zartar musu da hukuncin kisa da yawansu ya kai 1,281 suna nan an ajiyesu ne a wuraren ajiyan mutane guda 26 dake fadin kasar, haka zalika laifuka 33 ne suke janyo hukuncin kisa a kasar Malaysia.

“Daga ranar 22 ga watan Feburairu na shekarar 2019, akwai mutane 1,281 dake zaman jiran hukuncin kisa a kasar Malaysia, daga cikinsu akwai mutane 568 da suka fito daga kasashen waje, kasashe 43, inda kashi 21 na yan kasashen wajen yan Najeriya ne, kashi 16 Indonesia, 15 Iran, 10 India.

“Kashi 73 na mutanen sun aikata laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi ne, wanda sashi na 39(b) na kundin dokokin haramta shan munanan kwayoyi ta tanadar da hukuncinsa.” Inji AI.

Sai dai daga karshe kungiyar AI ta bayyana cewa bai kamata a yanke ma mutum hukuncin kisa saboda an kamashi da safarar miyagun kwayoyi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel