Boko Haram: Za mu ci gaba da neman taimakon kasashen duniya - Buhari

Boko Haram: Za mu ci gaba da neman taimakon kasashen duniya - Buhari

Kasar Najeriya ba za ta gushe wajen ci gaba da neman taimakon kasashen duniya domin ganin bayan kungiyar masu tayar da baya ta Boko Haram da sauran miyagun ababe na ta'ada da suka addabi kasar inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka zalika shugaban kasa ya sha alwashin cewa, gwamnatinsa ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da aminci a kasar nan ta hanyar tsarkake ta daga dukkanin wata barazana ta rashin tsaro da sauran ababe na ta'ada.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi watsi da nauyin da rataya a wuyanta ba na tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar nan kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Furucin shugaban kasar ya zo ne a ranar Laraba yayin bikin kaddamar da sabuwar lambar shekarar 2020 ta tunawa da dakarun sojin kasar nan da suka kwanta da dama.

Ya misalta dakarun da suka riga mu gidan gaskiya a matsayin babban rashi da kuma asara mai girman gaske wadda yaki da ta'addanci da sauran matsalolin tsaro suka haddasa salwantar rayukansu.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, akwai yiwuwar hukumomin Najeriya da na kasar Rasha za su hada gwiwa da juna domin inganta yanayin tsaron Najeriya musamman na mayakan tarzoma da ke gwagwarmaya da makamai tsawon shekaru a yanzu.

A ci gaba da fafutikar lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin Boko Haram da ya addabi kasar tsawon shekaru goma da suka gabata kawo wa yanzu, kasar Najeriya za ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta shafi harkokin tsaro da kasar Rasha.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta hautsine kan yadda ake daukan aiki a sirri a manyan ma'aikatu

Jakadan Najeriya a Rasha, Mista Steve Ugbah, wanda ya sanar da hakan a Juma'ar makon da ya gabata cikin birnin Moscow, ya ce za a cimma hakan ne a wata ganawa da ake sa ran za ta gudana tsakanin shugaba Buhari da Shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha.

Shugabannin biyu za su aiwatar da yarjeniniyar hakan ne a yayin wani taro tsakanin Rasha da kasashen Afirka, wanda zai gudana cikin wannan wata na Oktoba a birnin Sochi da ke yankin Bahar Aswad.

Haka kuma akwai batun yiwuwar Najeriyar ta sayo wasu manargartan kayan yaki da suka hadar da manya da kananan jirage gami da tankokin yaki daga Rashar a cewar jakadan na Najeriya, Steve Ugbah.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel