Yadda Yakin Iran Ya Jefa Amurka cikin Mummunan Yanayin Karancin ‘Makamai’
- Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu linzami na Patriot a Turai, yayin da yaƙin Iran ya sa aka tura da dama Gabas ta Tsakiya
- Jami’an tsaro sun ce ƙarancin Patriots na iya rage ikon NATO na kare ƙasashen Turai daga hare-haren makamai masu linzami na Rasha
- Sai dai NATO da Pentagon sun musanta cewa ƙarancin makaman ya kai matakin damuwa, suna cewa suna da isassun makamai domin kare ƙasashe da bukatun Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
WASHINGTON DC, US — Rundunar sojin Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu linzami na Patriot a Turai.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da yaƙin da Shugaba Donald Trump yake yi da Iran.

Source: Getty Images
Wani jami’in tsaron Amurka da ke Turai da wani jami’in NATO sun bayyana cewa ƙarancin ya haifar da damuwa kan yiwuwar raunin tsaron ƙasashen NATO, cewar AP News.
Fargaba kan karancin makaman Amurka
Jami’in tsaron Amurka ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne ƙarancin makamai masu linzami na Patriot da ake amfani da su wajen kare sararin samaniya.
Jami’in ya ce Patriots na iya kakkabo makamai masu linzami na Rasha masu saurin gaske, musamman makamai masu linzami masu bin hanya ta ballistic.
Jami’in NATO ya tabbatar da cewa yawan makaman Patriot da sojojin Amurka da na NATO ke da su a Turai ya yi ƙasa sosai.
Dukkan jami’an biyu sun yi magana ne ba tare da bayyana sunayensu ba, saboda suna tattaunawa kan batutuwan soja masu matuƙar muhimmanci.
Jami’in ya ce idan Rasha ta kai hari da makamai masu linzami kan hedikwatar soja ko tashar samar da wutar lantarki, NATO na iya fuskantar babbar matsala.
Ya ce Amurka ba ta da isassun Patriots a Turai da za su iya dakile ci gaba da kai hare-haren ballistic na Rasha.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun shiga fadar Sarki, sun kashe shi bayan korafi kan ta'adinsu a Niger
Wannan yanayi ya nuna illar da yaƙin Iran ya haifar, musamman bayan an tura wasu daga cikin makaman Amurka da ke Turai zuwa Gabas ta Tsakiya.
A can ne sojojin Amurka da ƙawayensu na yankin Gulf suka yi amfani da makamai masu linzami da dama, ciki har da Patriots, wajen dakile hare-haren Iran.

Source: Getty Images
Amurka ta rage yawan Patriots zuwa Ukraine
Ƙarancin Patriots ya fi bayyana a Ukraine, inda jami’an ƙasar ke neman ƙarin taimakon tsaron sama saboda makamai masu linzami na Rasha suna ƙara tsallake kariyarta.
Amurka ta bai wa Ukraine ɗaruruwan makamai masu linzami na Patriot tun bayan fara yaƙin, lamarin da ya rage wasu daga cikin kayayyakin da take da su, cewar Los Angeles Times.
NATO da Pentagon sun musanta ƙarancin makamai
Kanar Martin O’Donnell, babban kakakin sojan NATO, ya ce ba gaskiya ba ne cewa yawan makaman Patriot a Turai ya kai matakin “mai matuƙar tsanani”.
Ya ce NATO na da ikon dakile hare-hare, kuma tana da isassun makaman kare sararin samaniya domin kare kanta tare da bai wa Ukraine tallafi.
Martanin Iran kan sulhu da Amurka
A baya, an ji cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya yaba yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka a matsayin lamari mai tarihi.
Ya ce yarjejeniyar ta nuna murya ta al’umma da ta ki mika 'yancin ta ga barazana ko matsin lamba ta kudiri tsayin.
Yarjejeniyar ta hada da kawo karshen ayyukan soja, tattaunawa kan shirin nukiliya, sassauta takunkumi da sakin dukiyar Iran da aka rike da man fetur.
Asali: Legit.ng

