VeryDarkMan: Dan TikTok Ya Nunawa 'Yan Sanda Tsaurin Ido da Suka Gayyace Shi

VeryDarkMan: Dan TikTok Ya Nunawa 'Yan Sanda Tsaurin Ido da Suka Gayyace Shi

  • VeryDarkMan ya ce ba zai mika wa ’yan sanda hujjojin zargin da ya yi cewa jami’an tsaro na taimakawa wajen sace mutane da ayyukan ’yan bindiga ba
  • ’Yan sandan Najeriya sun gayyaci VeryDarkMan domin ya bayyana hujjojin zargin cewa wasu jami’ai na taimaka wa masu garkuwa da mutane
  • Duk da sukar hukumomin tsaro, VeryDarkMan ya ce ya kamata gwamnati ta inganta jin daɗin ’yan sanda domin ƙarfafa tsaron ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shahararren mai amfani da kafafen sada zumunta, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya ƙi mika wa rundunar ’yan sandan Najeriya hujjojin zargin da ya yi kan jami’an tsaro.

VeryDarkMan ya ce zai gabatar da hujjojin ne a gaban kotu idan aka gurfanar da shi, yana mai cewa lauyoyinsa a shirye suke su kare shi.

Kara karanta wannan

An shiga yanayin tashin hankali da wani bam ya tashi da mutane a jihar Zamfara

Verydarkman ya ki amsa gayyatar 'yan sanda
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu da VeryDarkMan
Source: Facebook

Dalilin da ya sa ya ki mika hujjoji

Verydarkman ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026.

Dan gwagwarmayar ya bayana cewa ba zai ba ’yan sanda hujjojin da suke nema ba kan zarge-zargen da ya yi.

Ya ce idan rundunar ta yi amanna cewa zarge-zargensa laifi ne, to ta gurfanar da shi a kotu, inda zai gabatar da hujjojin da yake da su.

“Ba zan ba ’yan sanda hujjoji na ba. Me ya sa zan yi hakan? Ya kamata a gurfanar da ni a kotu, kuma zan gabatar da su a can,” in ji shi.

Meyasa 'yan sanda suka gayyaci Verydarkman?

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta gayyaci VeryDarkMan ne bayan ya zargi wasu jami’an da ke aiki a wuraren binciken ababen hawa da gano masu kuɗi tare da mika bayanansu ga masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Abin mamakin da Bashir El Rufa'i ke gani idan ya ziyarci babansu da ke tsare

Rundunar ta bayyana zargin a matsayin mai matuƙar nauyi da kuma wanda ba a tabbatar da shi ba, tana mai cewa irin waɗannan kalamai na iya rage amincewar jama’a da hukumomin tsaro.

Sai dai rundunar ta ce idan Otse yana da sahihan hujjoji, za ta duba su tare da gudanar da bincike cikin gaggawa.

VeryDarkMan ya ci gaba da zarge-zarge

Duk da gayyatar, VeryDarkMan ya tsaya kan zargin cewa wasu hukumomin tsaro na da hannu wajen ci gaba da matsalar garkuwa da mutane, ’yan bindiga da ta’addanci a Najeriya.

Ya zargi ’yan sanda, sojoji, hukumar shige da fice da kwastam da sanin wasu abubuwan da ke taimakawa wajen dorewar matsalar tsaro.

Ya kuma tambayi dalilin da ya sa matsalar rashin tsaro ke ci gaba duk da makudan kuɗaɗen da gwamnati ke warewa domin yaki da ita.

VeryDarkMan ya ce ba zai ba 'yan sanda hujjoji ba
Martins Otse da aka fi sani da VeryDarkMan Hoto: Verydarkblackman
Source: Facebook

Ya nemi a inganta jin daɗin ’yan sanda

Duk da sukar da yake yi wa hukumomin tsaro, Martins Otse ya ce ya fahimci irin mawuyacin yanayin da jami’an ’yan sanda ke aiki a ciki.

Ya yi kira ga gwamnati da ta inganta walwala da yanayin aiki na jami’an tsaro, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya bayyana 'barayin' da yake fafatawa da su a zaben 2027

“Babu walwala ga ’yan sandan Najeriya. Idan kuna son a ƙarfafa tsaron Najeriya, dole ne ku kula da ’yan sandanmu,” in ji shi.

An kai dan TikTok gidan yari

A wani labarin kuma, kun ji cewa ann gurfanar da wani dan TikTok, Ademola Abiodun, wanda aka fi sani da DJ Chicken, a gaban Kotun Majistare da ke jihar Legas.

Bayan gurfanar da shi, an kai shi gidan yari bisa zargin yi wa Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, barazanar kisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng