Yan Sanda Sun Shammaci Ƴan Bindiga Suna Shirin Satar Kaya a Tirela, Sun Kashe 17

Yan Sanda Sun Shammaci Ƴan Bindiga Suna Shirin Satar Kaya a Tirela, Sun Kashe 17

  • Rundunar ’yan sandan Zamfara ta ce ta kashe ’yan bindiga 17 bayan jami’an tsaro sun yi musayar wuta da su
  • ’Yan bindigar sun kai hari kan motocin kasuwanci biyu, inda suka kashe direbobi da fasinjoji bakwai, suka raunata wasu
  • Rundunar ta ce jami’an tsaro sun kaddamar da samame kan maboyar ’yan bindigar, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto fasinjojin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rundunar ’Yan Sandan Zamfara ta samu gagarumar nasara a wani samame, inda ta ce ta kashe ’yan bindiga 17 dauke da makamai a jihar.

A ranar 25 ga Agusta 2026, da misalin karfe 4:05 na yamma, rundunar ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua.

Yan sanda sun kashe ƴan bindiga 17
Sufeta-janar na ƴan sanda, Rilwan Disu yana jawabi. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

’Yan bindigar sun bude wuta kan direbobi da fasinjoji ba tare da nuna bambanci ba, sannan suka tare wasu motocin haya guda biyu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Neja: Bayan umarnin Tinubu, an gano abin da yan sanda ke yi don ceto masallata da aka sace

Yan bindiga sun harbe direban mota

Daya daga cikin motocin, Sharon da ba shi da lambar rajista, Alhaji Halilu Namadi ne ke tukinsa daga Taloka zuwa Gwagwalada, Abuja.

Dayan motar kuma bas ce ta Hukumar Sufuri ta Jihar Sokoto, SSTA, mai lamba LV 94, wadda Sanusi Musa ke tukawa zuwa Kaduna da Abuja.

A lokacin harin, ’yan bindigar sun harbe direban Sharon har lahira, lamarin da ya sa motar ta rasa iko, ta kife ta kuma fita daga hanya.

Haka kuma, ’yan bindigar sun harbe fasinjoji shida, wadanda suka kunshi maza hudu da mata biyu, har suka mutu.

Bayan samun rahoton gaggawa, Kwamandan ’Yan Sandan Tsafe ya tattara jami’an sashen VCRU tare da jagorantar su zuwa wurin da lamarin ya faru.

An kashe yan bindiga a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda jami'an tsaro suka kashe yan bindiga

Da misalin karfe 6:45 na yamma a wannan rana, ’yan bindigar ta sake kai hari a kauyen Magazu da ke karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan bindiga da yawa sun baƙunci lahira a jihar Sakkwato

A yayin harin, wata harsashi da ta bace ta samu Lawali Muazu, mai shekaru 35, mazaunin kauyen Magazu, cewar Daily Post.

A wani samame na gaggawa, jami’an ’yan sanda da sojoji sun bi sawun ’yan bindigar da suka tsere zuwa babbar hanyar Funtua zuwa Gusau.

’Yan bindigar sun yi yunkurin tare wata motar dakon kaya da ke dauke da kayan abinci domin kwace kayanta.

Da suka ga jami’an tsaro suna zuwa, ’yan bindigar sun yi kokarin tserewa, amma jami’an suka bude musu wuta.

Musayar wutar ta kai ga kashe ’yan bindiga 17, yayin da wasu da dama daga cikinsu suka samu raunukan harbin bindiga.

Bam ya kashe mutane a Zamfara

An ji cewa rahotanni sun nuna cewa mutane biyu sun mutu bayan wani abin fashewa da ake zargin bam nd ya tashi a hanyar Gurusu-Gwashi ta jihar Zamfara.

Majiyoyi daga yankin da lamarin da auku sun bayyana cewa ana zargin wani babur ne ya taka bam ɗin da aka binne a ƙasa a Bukuyyum.

Dakarun rundunar sojoji sun ci gaba da sintiri da mamaye yankin domin hana sake kai makamancin wannan hari da kuma bincike wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.