Iran Ta Shawarci Ƙasashen Musulmi, Ta Tuna Masu yadda Annabi SAW Ya Rayu

Iran Ta Shawarci Ƙasashen Musulmi, Ta Tuna Masu yadda Annabi SAW Ya Rayu

  • Shugaban Iran ya yi kira ga ƙasashen Musulmi su ƙara haɗin kai, tare da haɗa kai wajen tabbatar da tsaron yankin
  • Pezeshkian ya ce bai kamata wata ƙasar Musulmi ta bari a yi amfani da ƙasarta wajen kai hari kan wata ƙasar Musulmi ba
  • Ya kuma ce ƙasashen Musulmi su ƙarfafa haɗin gwiwar kimiyya da tattalin arziki, tare da taimakawa Falasɗinawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga ƙasashen Musulmi da su ƙara haɗin kai, tare da yin hadin gwiwa wajen samar da tsaron yankinsu.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin taron ƙasa da ƙasa karo na 40 kan haɗin kan Musulmi da aka gudanar a Tehran.

Iran ta shawarci kasashen Musulmi
Dan Sarkin Saudiyya, Muhammad Bn Salman da Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran. Hoto: Inside the Haramain, Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Ya ce bai kamata kare Iran ya kasance ana kallonsa a matsayin ƙiyayya ga ƙasashen Musulmi ko maƙwabta ba, cewar Anadolu Ajansi.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya ba Hausawa, Fulani shawara da alakarsu ke neman baci

Abin da Iran ke bukata daga kasashen Musulmi

Pezeshkian ya ce Iran na maraba da ƙasashen maƙwabta domin samar da tsarin tsaro na bai ɗaya a yankin.

Ya jaddada cewa wannan yunƙuri bai samo asali daga rauni ba, illa dai daga darussan da Iran ta koya sakamakon yaƙi.

Ya ce:

“Kare Iran ba yana nufin kasancewa maƙiyin ƙasashen Musulmi da maƙwabta ba, bai kamata wata ƙasar Musulmi ta bari a yi amfani da ƙasarta a matsayin wurin kaddamar da hari kan wata ƙasar Musulmi ba.
“Bai kamata wata ƙasar Musulmi ta nemi tsaronta ta hanyar jefa maƙwabtanta cikin rashin tsaro ba."
Iran ta tuna wa kasashen Musumi rayuwar Annabi SAW
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Shawarar Iran ga kasashen Musulmi

Pezeshkian ya kara da cewa hakan ba ya nufin ƙasashen su kasance da manufofin ƙasashen waje iri ɗaya.

A cewarsa, haɗin kan tsaro yana nufin amfani da “hikimar gama-gari” wajen magance matsalolin yankin da kare ƙasashen juna.

Shugaban Iran ya kuma yi kira da a ƙara haɗin gwiwar kimiyya da tattalin arziki tsakanin ƙasashen Musulmi domin samun ci gaba, cewar Aljazeera.

Kara karanta wannan

Kebbi: Malami ya kafa kwamitin kamfen mai mutum 600 domin kifar da APC

Ya ce masana kimiyya daga ƙasashen Musulmi ya kamata su gudanar da ayyukan bincike tare, yayin da jarin cikin duniyar Musulmi ya rika yawo tsakanin ƙasashenta.

Pezeshkian ya ce ƙasashen Musulmi sun shafe shekaru suna tattauna kan maƙiyansu na bai ɗaya, amma yanzu lokaci ya yi da za su mai da hankali kan makomarsu.

Ya kara da cewa:

“Wannan shi ne matakin da ra’ayin haɗin kai ya kai wajen gudanar da mulki, idan muna son yin magana kan haɗin kan duniyar Musulmi, dole ne mu sake gina tare da ƙarfafa haɗin kan cikin al’ummominmu kullum."

Ya tambayi ko ƙasashen Musulmi za su iya magance bambance-bambancensu, tare da kare juna daga zubar da jini da haɗa kasuwanninsu.

Shugaban ya kuma tambayi ko za su iya yanke shawara kan muradunsu na bai ɗaya da kansu, maimakon barin wasu su yanke musu shawara.

“Wannan shi ne abin da Annabi ya aikata a Madina, kuma Imam da aka shahadantar ya dage a kai tsawon shekarun da ya jagoranci al’umma, haɗin kai ba dabara ce ta wucin gadi ba; shi ne hanyar dabarun Musulunci."

Kara karanta wannan

Ba yadda ake tsammani ba, gwamna ya fadi silar rashin tsaro a yankinsa

- In ji Pezeshkian

UAE ta yanke alakar kasuwanci da Iran

A baya, an ji cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da duk wata huldar kasuwanci da Iran, sakamakon hare-haren da take zargin kasar.

Matakin ya zo ne bayan karewar yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, wadda aka tsara domin bude kawo karshen yakin.

Rahotanni sun ce Iran na nazarin wasu hanyoyin fadada yakin, ciki har da kai hari kan sansanonin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.