Bai wa mata lasisin tuki da sauyi 7 da masarautar Saudiya ta kawo a bangaren nishadi

Bai wa mata lasisin tuki da sauyi 7 da masarautar Saudiya ta kawo a bangaren nishadi

Duba da kallon da ake yi mata a matsayin tsuhen daular musulunci kuma mai tsaurin ra'ayi wajen riko da akida da kuma al'ada, wasu sauye-sauye da ke ci gaba da gudana a kasar Saudiya a bangaren nishadi na ci gaba da barin baya da kura.

Ana iya tuna cewa a baya-bayan nan ne aka sanar da zuwan mawakiya Nicki Minaj saudiya domin baje kwazon sana'arta, lamarin da babu shakka ya janyo rudani da ce-ce-ku-ce a duniya musamman a kafofin watsa labarai da zaurukan sada zumunta.

Bangarori da dama na ganin cewa, Yarima Muhammad Bn Salman mai jiran gado ne ke kawo wadannan sauye-sauye a kasar musamman a bangaren nishadantarwa kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito.

A watan Fabrairun 2018 ne gwamnatin Saudiya ta kudirci ware zunzurutun kudi na kimanin dala biliyan 64 da manufar bunkasa masana'antunta na nishadantar wa cikin tsawon shekaru 10 masu zuwa.

Duk da irin suka da nuna rashin goyon baya daga bangarori da dama musamman mabiya addinin musulunci, Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya ya ayyana kudirinsa da cewa yana muradin mayar da Saudiyya a"matsayin kasa mai sassaucin ra'ayin addini tare da bude kofa ga dukkanin addinai da al'adu da mutanen duniya".

Ga dai jerin wasu muhimman sauye-sauye da yariman ya kawo a bangaren nishadantarwa wanda a baya suka haramta a kasar

1. Halasta bude gidajen kallon fina-finai wato sinima

2. Bayar da lasisin tarukan casu

3. Dawo wa da halascin bai wa mata izinin tuki

4. Bude gidajen rawa da kade-kade

5. Halasta kallon 'yan kokawa da wasan dambe wato Wrestling

6. Bai wa mata lasisi zuwa kallon kwallo

7. Tseren keken mata zalla

8. Halasta gwamutsar mata da maza yayin taron murnar cikar masarautar Saudiyya shekaru 87 da samun 'yanci, wanda aka gudanar a watan Satumbar 2017 cikin farfajiyar filin wasanni na Sarki Fahad da ke birnin Riyadh.

KARANTA KUMA: Hukumar NYSC ta tsawaita hidamar masu bautar kasa 52 a Kano

A na iya tuna cewa a ranar Lahadi ne kasar Saudiyya ta sanar da cewa daga yanzu baki mabanbanta jinsi wato namiji da mace ka iya kama dakin Otal daya koda kuwa babu aure a tsakanin su.

Wannan shine karo na farko da kasar Saudiyya ta bayar da irin wannan dama kuma ta yi hakan ne domin bai wa baki masu yawon bude ido damar ziyartar kasar da manufar yawon bude ido da shakata wa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng