Jihar Kaduna
Majalisar dokokin jahar Kaduna ta kammala aiki a wata kudurin doka wanda ta kirkireshi domin kawar da talauci a tsakanin al’ummar jahar Kaduna, kamar yadda majalisar ta bayyana da kan ta a ranar juma’a.
Shehu Sani ya yi kira ga gwamnonin Arewa kan cewa lokaci ya yi da ya kamata su farka daga barci, su san yadda za a kawo karshen hare-haren yan bindiga a yankin ko kuma a wayi gari wata rana a ce babu ma yankin Arewan gaba daya.
Nasir El-Rufai, Gwamnan jihar Kaduna, ya nemi gafarar mazauna kauyukan kananan hukumomin Igabi da Giwa na jihar a kan harin da aka kai musu wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 50.
A kalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a wasu kauyukan jihar kaduna. Mutane da yawa sun samu miyagun raunika a kauyukan kananan hukumonin Igabi da Giwa da ke jihar
Gagarumar gobara ta lashe gidan rediyon Freedom da ke jihar Kaduna a sa'o'in farko na ranar Lahadi. An gano cewa wutar ta samo asali ne daga gobarar da ta tashi daga wajen ajiye na'urar samar da wutar lantarki. Jaridar Daily Trust
Masu garkuwa da mutanen biyu da dakarun sojin suka kama sune; Bala Yunusa (wanda aka fi sani da Katako), dan asalin jihar Kaduna mai shekaru 35 da Idris Iliyasu (wanda aka fi sani da Dan Ikara), mai shekaru 37, dan asalin karamar
Wata kotun Majistare a jahar Kaduna ta tsare wani Muhammad Isah kan zargin lalata da kananan yaransa mata su biyu. Justis Musa Lawal na kotun Majistare ya kuma dage sauraron shari’an zuwa ranar 30 ga watan Maris 2020.
Sabon kakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, Tanimu Zailani ya bayyana yadda aka yi har ya dare wannan mukami bayan tsohon kaakakin majalisar, Aminu Abdullahi Shagali ya yi murabus a ranar Talata.
Ma’aikatar sharia ta gwamnatin jahar Kaduna ta gurfanar da wani likitan bogi mai suna Sa’idu Ahmed a gaban kotun majistri a kan tuhumarsa da take yi da yin sojan gona tare da kirkirar da amfani da takardun karatu na bogi.
Jihar Kaduna
Samu kari