Harin 'yan bindiga: Ku yi hakuri, na gaza baku kariya - El-Rufa'i ya nemi afuwa

Harin 'yan bindiga: Ku yi hakuri, na gaza baku kariya - El-Rufa'i ya nemi afuwa

Nasir El-Rufai, Gwamnan jihar Kaduna, ya nemi gafarar mazauna kauyukan kananan hukumomin Igabi da Giwa na jihar a kan harin da aka kai musu wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 50.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa El-Rufai yana kan hanyarsa ta zuwa kauyukan da aka kai wa harin.

Wani mafarauci ya sanar da VOA Hausa cewa 'yan bindigar sun kai hari kauyukan ne a ranar Lahadi, inda suka kashe mazaunan yankin da dama tare da bankawa gawawwakin wuta.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ali Janga ne ya raka gwamnan inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ba za ta taba yin ciniki da 'yan bindigar ba.

"Idan ba don taimakon jami'an tsaro ba, da sun yi nasarar karar da kauyukan tas," Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar kamar yadda El-Rufai yace.

"Na zo ne don bada hakurin rashin ba ku cikakkiyar kariya. Muna iyakar kokarinmu wajen kare aukuwar irin wannan lamarin. Ku yafe mana.

Harin 'yan bindiga: Ku yi hakuri, na gaza baku kariya - El-Rufa'i ya nemi afuwa
Harin 'yan bindiga: Ku yi hakuri, na gaza baku kariya - El-Rufa'i ya nemi afuwa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa

"Muna iyakar kokarinmu kuma muna fatan za mu shawo kan ta'addanci saboda jami'an tsaro na kan lamarin. A jihar Kaduna, muna da yawa. Idan jami'an tsaron suka rufo wani wajen, sai 'yan ta'addan sun fada wani wurin." ya kara da cewa.

Gwamnan ya tabbatar da cewa aikin mulkinsa ne karar da maharan.

"Alhakin karar da maharan ya rataya a wuyanmu ne kuma har sai mun aika su ga mahaliccinsu ne hankulanmu zasu kwanta," ya ce.

"Hukumomin tsaron na iya bakin kokarinsu amma suna samun babbar matsala ta shiga kauyuka saboda matsalar tituna. Amma ina matukar godiya ga rundunar sojin Najeriya, 'yan sanda da jami'an tsaro na farin kaya ta yadda suka yi gaggawar kai dauki." ya kara da cewa.

El-Rufai yayi kira ga jama'ar jihar da su ci gaba da hakuri tare da kara sa ido don taimakon gwamnati da jami'an tsaro wajen cin nasara a yakar 'yan ta'addan.

A bangaren Ibrahim Damu, dagacin Kerawa, yayi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel