Alkali ta dakatar da shirin Gwamnatin Kaduna na rusa dinbin gidaje a Chikun

Alkali ta dakatar da shirin Gwamnatin Kaduna na rusa dinbin gidaje a Chikun

Babban kotun jihar Kaduna ta bada umarnin dakatar da ruguza gidaje fiye da 2000 da gwamnatin Mai girma Malam Nasir El-Rufai ta ke shirin yi a cikin jihar.

Alkali mai shari’a Binta Zubairu ce ta yanke wannan hukunci kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 8 ga Watan Maris. Za a cigaba da shari'ar a karshen Wata.

Hukumar KASUPDA mai kula da tsarin gine-ginen da cigaban Biranen jihar ta nemi ta rusa gidajen mutane da-dama a Unguwannin Nisi da Tasu a Chikun.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa kwanaki KASUPDA ta bada wa’adin ruguza gidaje akalla 2000 da ke wadannan Unguwanni da ke kunshe da mutane 10, 000.

Shugaban hukumar KASUPDA, Isma’il Umaru Dikko, ya rubuta takardar da aka aikawa Mazauna wadannan wurare ana sanar da su za a rusa gidajen da su ke ciki.

KU KARANTA: KASUPDA ta rusa wasu gidajen jama'a akalla 300 a Kaduna

Alkali ta dakatar da shirin Gwamnatin Kaduna na rusa gidaje a Chikun

Akwai gidaje 2000, coci 25 da makarantun boko 14 a tsakanin Nisi da Tasu
Source: Depositphotos

KASUPDA ta bayyana cewa an yi wadannan gini ne ba tare da bin ka’ida ba, inda aka shiga kan fegin masana’antu, sannan kuma ba a samu takardun gwamnati ba.

A dalilin wannan laifi wanda ya sabawa sashe na 60 (2) na dokar jihar Kaduna na 2018, KASUPDA ta ba jama’an wurin kwanaki 21 da cewa su tattara su tashi daga Yankin.

Sakamakon wannan umarni na gwamnatin El-Rufai ne Mutanen Yankin su ka garzaya kotu, su na rokon Alkali ya hana hukumar KASUPDA rusa gidajen da su ke ciki.

Zubairu ta bada umarni a dakata tukuna da wannan aiki na ruguza gidajen mutane. Alkalin ta bukaci hukumomi su jira har sai zuwa lokacin da aka gama shari'a a kotu.

Lauyan da ke kare wadannan mutane ya shaidawa ‘Yan jarida cewa Mazauna yankin su na da takardun CofC na zama. Yanzu dai an dage karar zuwa karshen Watan nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel