Masu Amfani da Layukan Sadarwa Sun Ci Bashin N4.6bn a Shekarar 2025

Masu Amfani da Layukan Sadarwa Sun Ci Bashin N4.6bn a Shekarar 2025

  • Rahotanni sun bayyana cewa masu amfani da layukan waya a sun ci bashin kati na kusan tiriliyoyin Naira a shekarar 2025
  • Afirka ta bayar da sama da 94% na duk bashin kati da kamfanin ya raba, lamarin da ya nuna karuwar matsin tattalin arziki
  • Karuwar bashin kati da kananan rance ta taimaka wajen habakar kudaden shiga duk da karin hadarin rashin biya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kamfanin fasahar kudi na Optasia ya bayyana cewa miliyoyin masu amfani da layukan waya sun ci bashin tiriliyoyin Naira a 2025

An tabbatar da cewa mutanen Afirka sun ci bashin kati daga kamfanonin sadarwa da ya kai dala biliyan 3.18, kimanin Naira tiriliyan 4.6, a 2025.

Yawan harsunan da aka ci daga kamfanonin sadarwa a 2026
Wasu mutane da ke amsa waya ta hanyar amfani da layukan kamfanonin sadarwa. Hoto: Uniq, Brand Image, Kliq Trend.
Source: UGC

Bambancin cin bashi a shekarun 2024 da 2025

Adadin ya karu da kashi 12.3 idan aka kwatanta da dala biliyan 2.83 da aka bayar a shekarar 2024, abin da ke nuna karin dogaro da irin wannan sabis, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Masifa ta fada Amurka, jirgin soji ya fado, jama'a da sojoji sun mutu

Afirka ce ta mamaye wannan kasuwa, inda aka bayar da dala biliyan 2.99 daga cikin jimillar bashin katin, wanda ya zarce kashi 94 cikin 100.

Bashin kati da a baya ake dauka a matsayin mafita ta dan lokaci, yanzu ya zama wata muhimmiyar hanya ta gudanar da kira, amfani da bayanan intanet da mu'amalolinta.

Optasia na aiki a kasashe sama da 25 ciki har da Najeriya, Ghana, Masar da Habasha, inda take bayar da bashin kati da kananan rance.

Kamfanin na amfani da fasahar nazarin halayen masu amfani domin tantance cancantar su kafin amincewa da bayar da bashi.

Bangaren ba da kananan rance na kamfanin ya bayar da dala biliyan 2.30 a shekarar 2025, fiye da ninkin adadin shekarar 2024.

Afirka ta bayar da gudunmawar dala biliyan 1.41 a bangaren kananan rance, abin da ya tabbatar da matsayin Nahiyar a wannan fanni.

Yan Afirka sun ci bashin N4.6bn a 2025 kacal
Ofishin hukumar sadarwa ta NCC da ke Abuja. Hoto: Nigeria Communication Commission.
Source: Twitter

Yadda harkokin sadarwa ke bunƙasa a Afirka

Ribar kamfanin bayan cire haraji ta kai dala miliyan 43.13, yayin da Afirka ta samar da kusan kashi 89 na kudaden shigarsa.

Masana sun ce wannan ci gaba yana nuna yadda harkokin sadarwa da ayyukan kudi ke kara hade guri guda a Afirka, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 1 da harin Yelewata, Lakurawa sun kashe fiye da mutane 15 a Kebbi

Sun bayyana cewa yawan masu amfani da wayoyin hannu ya fi na masu asusun banki, lamarin da ke bude damar kai rance ga wadanda ba su da isassun ayyukan banki.

A Najeriya, sabis na cin bashin kati da bayanan intanet na kara samun karbuwa saboda saukin samun kananan rance cikin gaggawa.

Gwamnatin tarayya ma na nazarin sauye-sauye domin bai wa karin kamfanonin fasahar kudi na cikin gida damar shiga kasuwar bashin kati.

Rahoton ya nuna cewa bashin da ke da alaka da kamfanonin sadarwa na daga cikin sassan tattalin arzikin zamani mafi saurin bunkasa a Afirka.

Sabis: MTN ya tura wa yan Najeriya kudi

A baya, an ji cewa kammfanin MTN ya rabawa mutane katin waya a layukansu domin biyan diyyar matsalar sabis da aka samu a watan Janairu, 2026.

Hakan ya biyo bayan umarnin da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ba kamfanonin saboda rashin karfin sabis.

Wani matashi, Zaharaddeen Hamisu ya nuna damuwarsa kan matsalar sabis, yana mai cewa tana hana matasa samun wata damar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.