Harin Kaduna: Gwamnonin Arewa su farka daga barci ko kuma a wayi gari babu yankin – Shehu Sani

Harin Kaduna: Gwamnonin Arewa su farka daga barci ko kuma a wayi gari babu yankin – Shehu Sani

Tsohon dan majalisa mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnonin Arewa kan cewa lokaci ya yi da ya kamata su farka daga barci, su san yadda za a kawo karshen hare-haren yan bindiga a yankin ko kuma a wayi gari wata rana a ce babu ma yankin Arewan gaba daya.

Sani ya bayyana cewa ‘yan bindiga na yin abun da suka ga dama a yankin Arewcin kasara, sannan maimakon a samu sauki abun sai gashi ya kara yin gaba.

“Musulmi da ake halakawa bai zama abin daga hankali ba domin shugabannin su ba su son su yi maganar da zai taba zuciyar gwamnati, su ko kiristoci, a kulli-yaumin suna fitowa su nuna fushin su da Alla-wadan su game da abinda ke faruwa na kashe-kashen mutane da ake yi.

Harin Kaduna: Gwamnonin Arewa su farka daga barci ko kuma a wayi gari babu yankin – Shehu Sani
Harin Kaduna: Gwamnonin Arewa su farka daga barci ko kuma a wayi gari babu yankin – Shehu Sani
Asali: Facebook

“Gaba daya gwamnonin Arewa suna tsoron su yi gaba-da-gaba da gwamnatin tarayya wajen fada mata gaskiya, alhali a nan ana ta kashe musu mutanen tare dayin garkuwa da su.

“Matsalar rashin tsaro a yankin Arewacin kasar na kara samun wajen zama ne a dalilin munafurcin da shugabannin yankin ke yi na kin fada wa gwamnati gaskiyar matsalolin da ake fama dasu. Sai a rika yi kamar komai lafiya lau ya ke.

“Idan ana kashe mutanen mu, ana garkuwa da su, sannan muka fito muka yi magana, sai gwamnati da ‘yan kanzagin ta su fito suna cewa wai siyasa ce, ba gaskiya ba.

KU KARANTA KUMA: An kama wata mata yar shekara 45 da ke safarar yara tare da yara 23 a Taraba

“Matsalar tsaro a Arewa ya zama annoba a yankin da kasa baki daya kuma ya zama abin tashin hankali ya yankin Afrika ta Yamma. Dole gwamnoni su hadu su samar da wani runduna, ko tsari don samar wa mutanen yankin tsaro wallahi, ko kuma duk mu zama abin tausayi,” in ji Shehu Sani.

A bangare daya kuma mun ji cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa bisa mummunar harin kisan kiyashi da wasu yan bindiga suka kai ma al’ummar jahar Kaduna a ranar Lahadi inda suka kashe sama da mutane 51.

Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa a bangaren watsa labaru, Malam Garba Shehu a ranar Litinin, wanda ya ce ta tabbata yan bindigan suna kai ma jama’an da ba su ji, ba su gani ba hari sakamakon matsin lamba da suke fama da ita daga wajen jami’an tsaro a dajin Birnin Gwari da Kaduru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel