Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutane 30 a wasu kauyukan jihar Kaduna

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutane 30 a wasu kauyukan jihar Kaduna

A kalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a wasu kauyukan jihar Kaduna. Mutane da yawa sun samu miyagun raunika a kauyukan kananan hukumonin Igabi da Giwa da ke jihar.

Kauyukan da abun ya shafa sun hada da Kerawa, Rago, Marina, Zariyawa, Hashimawa, Gidan Musa Saidu, da Unguwar Barau.

Duk da cewa hukumar 'yan sandan jihar har yanzu ba ta tabbatar da aukuwar lamarin ba, wani mazaunin karamar hukumar Giwa ta jihar, ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels cewa rundunar sojin Najeriya ce ta kai samame wajen 'yan ta'addan kuma ta kashe wasu daga ciki.

Majiyar ta kara da cewa, 'yan ta'addan sun kai musu harin ne a kokarinsu na daukar fansar rayukan 'yan uwansu da sojojin suka dauka. Sun zargi 'yan kauyen da ba jami'an tsaron bayanai a kan maboyarsu wanda hakan yasa suka yi musu kisan kiyashi.

A lokacin da ake rubuta wannan rahoton, rundunar sojin na ci gaba da yi wa 'yan ta'addar ruwan wuta a cikin dazuzzukan Giwa, Birnin Gwari da karamar hukumar Igabi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel