Gwakuru: Tafkin da macizai, kifaye da halittu daban-daban ke zaune lafiya a Kaduna

Gwakuru: Tafkin da macizai, kifaye da halittu daban-daban ke zaune lafiya a Kaduna

Gwakuru wani karamin tafki ne da ke can a yankin kudancin jihar Kaduna a karamar hukumar Kagarko. Tafkin ya kasance masamar ruwan sha ga mazauna wajen amma kuma akwai dumbin tarihi da abubuwan al'ajabi da ke kunshe da tafkin.

Wani abun mamaki kuwa shine yadda tafkin ko kadan baya bushewa komai rani ko kuma damina.

A ranar Lahadi ne jaridar Daily Trust ta gano cewa wannan tafkin bashi da wata hanyar shiga ko fitar ruwa. Tafkin na zagaye ne da manyan bishiyoyin da ke matukar kawata shi a yayin damina. Akwai ciyayi da suke kara wa wurin matukar kyau.

Ruwan tafkin bashi da kala, yana da matukar kyau don har kasan ruwan ake hangowa. Amma idan aka yi ruwan sama, ruwan na rikidewa ya koma kalar ruwan kasa. Ana samun kifaye masu matukar ban sha'awa tare da macizai da ke rayuwa a wajen.

Amma kuma mazauna yankin sun tabbatar da cewa suna diban ruwa da ayyukansu na yau da kullum ba tare da dabbobin sunyi musu komai ba.

Gwakuru: Tafkin da macizai, kifaye da halittu daban-daban ke zaune lafiya a Kaduna
Tafkin Gwakuru
Asali: Twitter

A kowacce shekara dai mazauna yankin kan yi bikin gyaran tafkin. Wannan bikin kuwa ya fada Lahadi ne inda aka samu zantawa da Sarkin Leman Sarkin Kagarko, Malam Sa'idu Madauci wanda ya bayyana cewa sun yi imanin cewa kifayen da macizan da ke tafkin duk aljanu ne.

DUBA WANNAN: Addu'ar da mahaifiyar Sanusi II ta zazzaga masa yayin da ta ziyarce shi (Bidiyo)

A yayin karin bayani a kan bikin, ya ce ana zuba wasu magunguna ne a tafkin da dadare, ana gobe za a yashe tafkin. "Wannan maganin na sa duk wani maciji aljani ya bar farfajiyar tafkin kafin mu fara yasar. Daga nan sai su bar wadanda basu da illa."

Malam Sa'idu Ibrahim ya ce duk wanda ya kashe ko ya ci kinfin tafkin Gwakuru ko maciji, tilas ne mutuwarsa. Ya kara da cewa duk wanda ya diba ruwa tafkin sannan ya samesa ya karba magani, toh kowanne ciwo ke damunsa zai samu waraka da izinin Ubangiji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel