Gobara ta babbake gidan rediyon 'Freedom'

Gobara ta babbake gidan rediyon 'Freedom'

Gagarumar gobara ta lashe gidan rediyon Freedom da ke jihar Kaduna a sa'o'in farko na ranar Lahadi. An gano cewa wutar ta samo asali ne daga gobarar da ta tashi daga wajen ajiye na'urar samar da wutar lantarki.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, wutar ta shafi dakin ajiye na'urar samar da wutar lantarki, babban ofishin talla, dakin taro, ofishin jami'an tsaro da kuma dakin direba.

An kara gano cewa, gidan rediyon mai zaman kan sa ya datse watsa shirye-shirye na wucin-gadi har zuwa karfe 10:45 na safiyar ranar Lahadin.

Gobara ta babbake gidan rediyon 'Freedom'
Gobara ta tafka barna a gidan rediyon 'Freedom'
Asali: Twitter

Gobara ta babbake gidan rediyon 'Freedom'
Ta'adin da gobara ta yi a gidan rediyon 'Freedom'
Asali: Twitter

Shugaban sashen ayyuka na gidan rediyon, Abubakar Jiddah Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce wutar ta fara ne da misalinn karfe 2:30 na safiyar Lahadi.

DUBA WANNAN: Zargin zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa

"Ina tunanin tsananin zafi ne daga kayan wutar ya kawo gobarar kuma har ta lashe ofisoshi biyar. Mun dakatar da shirye-shiryenmu har zuwa karfe 10:45 na safiyar Lahadi. Da izinin Ubangiji za mu ci gaba da ayyukanmu," a cewarsa.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa kayayyaki da kadarorin da gobarar ta lamushe sun kai na miliyoyin nairori.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel