El-Rufa'i zai fara biyan 'yan fansho sabon karin albashi daga watan Maris

El-Rufa'i zai fara biyan 'yan fansho sabon karin albashi daga watan Maris

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta fara biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi ga 'yan fansho a jihar biyo bayan sabunta tsohon tsarin biyan 'yan fansho da aka yi a cikin watannan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da Muyiwa Adekeye, mai bawa gwamna El-Rufa'i shawara a kan sadarwa da kafafen yada labarai, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.

A cewar jawabin, sabon tsarin zai rabauta 'yan fansho 11,511 wadanda zasu fara daukan N30,000 a karshen wata, sabanin tsohon albashinsu wanda bai kai ba.

Ya ce dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati sun samu sanarwa daga ofishin shugaban ma'aikata a kan kaddamar da sabon tsarin fanshon.

"Biyo bayan shawarar da majalisar zartarwa ta yanke a kan kara albashin 'yan fansho zuwa N30,000, shugabar ma'aikata, Bariatu Mohammed, ya bayar da umarni ga hukumomin gwamnati domin kaddamar da tsarin daga watan Maris, 2020," a cewarsa.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa umarnin ya bukaci dukkan hukumomi su bayar da hadin kai ga sabon tsarin da majalisar zartarwar ta amince da shi a kwanakin baya bayan nan.

Ya bayyana cewa gyaran albashin 'yan fanshon ya samo asali ne daga niyyar gwamnatin jihar Kaduna na ganin ta inganta walwala da jin dadin jama'arta, musamman ma'aikata da wadanda suka yi ritaya.

Takardar, mai dauke da kwanan watan ranar Laraba, 11 ga watan Maris, ta jaddada cewa bangaren zartarwa zai cogaba da kokarin inganta rayuwar dukkan mazauna jihar Kaduna.

Jawabin ya kara da cewa daga cikin 'yan fansho da zasu ci moriyar karin albashin, akwai wadanda a baya ake biyansu N3,000 kacal a wata.

Source: Legit

Online view pixel